KANO STATE FORUM

KANO STATE FORUM We are here to promote justice and that is our stance

Free CUPS Computer and ICT Training - Latest UpdateUPDATE IN ENGLISH:Fellow compatriots, I write to update you with our ...
08/09/2025

Free CUPS Computer and ICT Training - Latest Update

UPDATE IN ENGLISH:

Fellow compatriots, I write to update you with our progress as follows:

1. We are now fully engaged with the new 160 Computer and ICT experts that we hope to recruit to teach and mentor you Computer and ICT. We have sent them emails and most of them have responded favourably. By Sunday, 14th September 2025, all the experts interested in working with us would have signed a legally binding MoU contract with the CUPS Organisation. The MoU details the job specification, duration of the training, monthly salary, how payment is made and finally rules of disengagement, should the need arise (We hope and pray this doesn't happen).

2. We are also fully engaged with the CUPS syllabus translators into Hausa language. The latest comprehensive syllabus is 41 pages. It is being translated into Hausa language. We expect to get at least 5 fully completed accurate translations by Sunday, 14th September 2025. The best 3 translations will be shared free in all the CUPS Tutor groups.

3. Following a successful engagement with the new Computer and ICT experts, 18 of them will be immediately recruited to expand the classes to 20. Network stability is a significant deciding factor. Starting with 20 classes means we will have a cohort of 50,000 students (there are 2,500 students in each class). However, if the network proves stable, we may decide to increase the number of classes and recruit more tutors.

4. Just before we commence training, all students will be rearranged into 10 classes where the language of instruction will be purely English, and the other 10 classes will be bi-lingual (English and Hausa). It is entirely up to a student to chose which language class to belong to. We created this arrangement to overcome the language issues/challenges encountered by the 3MTT program, which led it its failure in some Northern states.

Thank God, we have made significant progress over the last 3 weeks. This explains my absence from Facebook. Please, keep praying for the success of this program. Fellow compatriots, I leave you in peace.

Dr. Idris Ahmed.
President CUPS.
07/09/2025.


BAYANI DA HAUSA:

Jama'a Barkanmu da warhaka. Ga sabon karin bayani kamar haka:

1. A yanzu haka, muna cikin cikakken hulɗa tare da sabbin ƙwararrun kwamfuta da na ICT, su 160, waɗanda muke fatan za mu ɗauke su don su koya muku ilimin kwamfuta da ICT. Mun aika musu da imel kuma yawancinsu sun ba da amsa mai kyau. Nan da ranar Lahadi, 14 ga Satumba, 2025, duk ƙwararrun masu son aiki da CUPS, za su sanya hannu kan kwangilar yarjejeniya (MoU) tare da Ƙungiyar CUPS. Yarjejeniyar MoU ta ƙunshi cikakkun bayanai game da yanayin aikin, tsawon lokacin karantarwan, albashi a kowane wata, yadda zamu biyasu albashi, da kuma ƙa'idodin rabuwa, idan har an samu akasi (Allah Ubangiji Ya kiyaye. Amin).

2. Hakanan kua muna cikin cikakken hulɗa tare da masu fassara manhajar karatun kwanfuta. Muna sa ran samun aƙalla cikakkun fassarori guda 5 daidai nan da ranar Lahadi, 14 ga Satumba, 2025. Zamu raba mafi kyawun fassarorin kyauta a cikin duk azuzuwa 20 na kwamfuta.

3. Bayan nasarar hulɗa tare da sababbin ƙwararrun kwamfuta da ICT, zamu dauki 18 daga cikinsu nan take don faɗaɗa azuzuwan zuwa 20. Zamu ƙara ɗaukar wasu sabbin malamai yayin da muke samun ci gaba. Fara horaswa da azuzuwa 20 yana nufin zamu fara da ɗalibai 50,000 (akwai dalibai 2,500 a kowani aji). Duk da haka, idan hanyar sadarwa ta tabbata (Network), toh muna iya yanke shawarar ƙara azuzuwan da ɗaukar ƙarin malamai.

4. Kafin mu fara horarswa, za a sake tsara duk ɗalibai zuwa azuzuwa 10 inda harshen koyarwa zai zama Turanci kawai, sauran azuzuwa 10 kuma za su kasance masu amfani da harsuna biyu (Turanci da Hausa). Ya rage wa ɗalibi ya zaɓi ko wane irin ajin harshe zai shiga. Mun ƙirƙiri wannan tsari ne don magance matsalolin harshe da shirin 3MTT ya fuskanta, wanda ya haifar da gazawar program din a wasu jihohin Arewa.

Tabbas, munyi gagarumar nasara a sati uku da s**a gabata. Wannan shine dalilin da yasa baku ganni a wannan dandalin ba. Toh Allah Ubangiji Ya datanmana. Amin Ya Rabbi. Jama'a kuci gaba da yi mana addu'an samun nasara akan wannan tafiya. Jama'a na barku lafiya.

Dr. Idris Ahmed.
President CUPS.
08/09/2025.

Sanarwa: CUPS Computer 🖥️ and ICT Training!Jama'a barkanmu da warhaka. Muna nan muna fama da tura muku emails dangane da...
11/06/2025

Sanarwa: CUPS Computer 🖥️ and ICT Training!
Jama'a barkanmu da warhaka. Muna nan muna fama da tura muku emails dangane da CUPS Computer and ICT Training.

Tun ranan Lahdi (8/6/2025) muka fara tura muku emails, toh amma har yanzu ba dukanku ne kuka sami email din ba. Munyi wa kamfanin GoDaddy korafi dangane da wannnan lamarin, sunyi mana bayanin cewa suna da wani tsari ne na tabbatar da cewa duk wata sabuwar kungiya irisnsu CUPS ko sabuwar kamfani da ke da kudurin tura email masu tarin yawa, toh sai sun tantance sakon da ke cikin email din babu malicious codes (virus), kuma sun tantance cewa email addresses din (16,000) ba satansu CUPS tayi ba domin cutar da al'umma. Toh wannan tantancewan shine yasa abubuwa basa gudana yadda muke bukata.

Insha Allah kowa zai sami email dinsa kafin ranan Lahdi, 15/6/2025. Email din yana cike da bayanan abubuwa kamar haka:

1. Lambar class naku (akwai ICT Class 1 zuwa ICT Class 😎
2. Sunan Malami mai bada training a class naku.
3. Link na website inda zakuyi ragista na karshe domin yin training.
4. Link na website inda zakuyi training.
5. Username da password.
6. Link na WhatsApp group na ajinku domin tattaunawa da malaminku da sauran dalibai.
7. Link na Telegram group na ajinku domin tattaunawa da malaminku da sauran dalibai.

A zagaye na farko, mun tura emails wadandanda babu wadannan bayanai da na lissafa a sama. Ku kwantar da hankalinku. Zamu sake tura muku email a zagaye na biyu, wadanda ke da bayanan.

Jama'a ku ci ganba da duba email naku. Kuma ku ci gaba da bibiyanmu a wannan dandalin da kuma dandadlinmu na Telegram domin samun karin bayani.

Na barku lafiya.

Dr. Idris Ahmed.
CUPS.
11/06/2025.

24/04/2025

Ni Ban Hangi Mafita Ga Arewa Ba!
Jama'a barkanmu da warhaka. A cikin makonni uku da s**a gabata zuwa yau, ina ta nazari akan shige da ficen yan siyasanmu na Arewa. Idan banda kalilan a cikinsu, ni banga alaman mutannennan don Allah sukeyin siyasan ba.

Jama'a ku dubi yadda yankinmu na Arewa ta dau zafi ta yamutse domin bakin talauci da rashin tsaro, amma yawancin yan siyasanmu damuwarsu itace wace jamiyya ce zasu shiga domin cin zaben 2027. Allah wadan naka ya lalace!

Wallahi, idan bamu yi hankali ba, babu wani zabe da za'ayi mai inganci a 2027, domin wannan bakin azzalumin shugaban kasa ya san irin barna da ya yiwa Najeriya da al'ummanta, saboda haka zai gwamnace gwara ta tafasa ta kone akan ya rasa kujerarsa!

Ganin yadda tsaro ya tabarbare a Arewa, ya kamata ace duk yan siyasanmu na Arewa sun hada kai domin samarwa Arewa mafita. Amma idan banda irinsu Major Al-Mustapha, Sanata Ali Ndume da gwanonin Borno, Katsina da Zamfara, ban ji wani ya fito fili yana kalubalantar gwamnatin Tinubu akan rashin tsaro a Arewa ba!

Munafukai irin su Nuhu Ribadu da gwamnan Jihar Sokoto, wadannan babu kunya babu tsoron Allah, fitowa sukeyi a gaban Jama'a suna zuka karya cewa tsaron Arewa ya inganta a karkashin Tinubu! Wannan ba daidai bane, kuma Allah Ubangiji zai yi musu kamu mai tsanani!

Sauran yan siyasa, sanatocinmu da yan majalisan wakilanmu da ke Abuja, shiru kakeji kamar an shuka dusa. Kowa ta kansa da iyalinsa yake yi.

Toh Jama'a, Allah Ubangiji ya kawo mana mafita, ba don halinmu ba, kuma ba don ayyukanmu ba. Amin. Amma ni ban hangi mafita ga Arewa ta hannun yan siyasanmu ba.

Jama'a na barku lafiya.

Dr Idris Ahmed.
CUPS.
24/4/2025.

Sanarwa Daga CUPS!Jama'a barkanmu da warhaka. Barkanmu da safiyan Juma'a. Allah Ubangiji Ya sa muci dinbin Alherinsa da ...
31/01/2025

Sanarwa Daga CUPS!
Jama'a barkanmu da warhaka. Barkanmu da safiyan Juma'a. Allah Ubangiji Ya sa muci dinbin Alherinsa da ke tattare da wannan ranan. Amin Ya Rabbi.

Jama'a muna aiki tukuru domin tabbatar da cewa mun fara Computer/ICT Training a kan lokaci. Insha Allah zamu fara nan da sati biyu.

Alama ya nuna cewa zamu fara da Jihar Kano. Domin itace jihar da tafi kowace jiha a Arewa yawan al'umma, mussaman matasanmu wadanda zasu bukaci wannan training. Bayan mun kammala Kano zamu shige wata jihar kuma.

Zamuyi amfani da online training domin saukakawa masu training. Zamuyi amfani da website na CUPS da kuma dandalinmu na CUPSTV. Toh amma wajen practicals, dole ne mutane su halarci computer laboratory inda zamu dauki haya.

Zamuyi iyakacin kokarinmu mu tabbatar cewa bayan training matasanmu da s**a kammala sun sami certificate, wadda Jami'a ce zata bayar. Yin hakan zai inganta musu samun aiki.

Dandalinmu na CUPS WhatsApp ya cika makil, kuma akwai mutane 950 suna kan layi suna jiran shiga, toh amma kuna iya binmu ta dandalin Telegram domin duk bayanai da mukeyi a WhatsApp muna yinsu a Telegram. Ku dubi sashin comments, akwai link na Telegram din.

Na barku lafiya.

Dr Idris Ahmed.
CUPS.
31/01/2025.

28/01/2025

Jama'a barkanmu da warhaka. Ba kyautan kudi (dollar) ba, Wallahi ko duk duniya Bola Ahmed Tinubu zai bani, wai naje na hallarci wani taron karantun Al'kurani, toh ba zanje ba. Ga dalilai na kamar haka:

1. Akwai babban hatsarin yiwa Allah izgili wajen yin wannan taron, domin Al'kurani Kalmar Allah Madaukakin Sarki ne, ba abin wasa ba!

2. Tinubu barawone, ya saci dukiyan Jama'an Jihar Lagos fiye da duk wani sata da gwamna ya taba yi a tarihin Najeriya. Babban barawo ba mutumin kirki bane mai nagarta, wadda zai tara Mahaddasan Al'kurani har ma a saurareshi.

3. Duniya ta shaida cewa shine mutum na uku da yafi kowa almundahana a duniya.

4. Tinubu mayaudari ne, butulu, maci amana. Al'ummanmu na Arewa sune s**a zabeshi ya zama shugaban kasa. Amma da cin zabe, tun ba'a rantsar da shi ba, ya garzaya Faransa ya karbo kwangilan rushe Arewa da al'ummanta.

5. Taron Qur'anic Convention (Festival) ba don Allah Tinubu ya shiryata ba. Taro ne na cimma wata manufa ta siyasa.

6. Allah Ubangiji Tsarkakakken Sarki ne, kuma baya karban aiki ko ibada wadda ba tsarkakakkiya ba.

7. Daga karshe, an kiyasta cewa Tinubu zai kashe Naira 35 billion don wannan taron. Allah zai tambayi Tinubu da duk wadda ya halarci wannan taron don me gwamnatin tarayya bata kashe makudan kudadennan wajen inganta tsaro, rage talauci da tallafawa talakawa ba, domin gwamnatin ta gaza kwarai da gaske a wadannan fannonin.

Na barku lafiya.

Dr. Idris Ahmed.
CUPS.
28/01/2025.

26/01/2025

BABBAN MATSALAR DA KE FUSKANTAR YANKIN MU NA AREWA

Marubuci ✍️ Musa Kazaure.

Yankinmu, ya dogara sosai kan aikin gwamnati da siyasa. Wannan dogaron ya jefa mu cikin wani hali na rashin fahimtar cewa duk wani matsayi ko albashi daga aikin gwamnati da siyasa na ɗauke da iyaka, wato ba na har abada ba ne. Hakan ya sanya zuciyoyinmu s**a mutu, ba ma son wahala, domin mun saba da samun kuɗi cikin sauƙi ta hanyar siyasa ko aikin gwamnati.

Wanda yake da hankali da tunani, idan ya dubi baya, zai lura da yadda iyayenmu da s**a dogara kacokan da aikin gwamnati ke rayuwa bayan sun yi ritaya. Kuma hakazalika, waɗanda s**a dogara da siyasa kaɗai, yanzu da ba su da iko, ya kamata mu duba irin rayuwar da suke ciki. Wannan ya zama darasi gare mu gaba ɗaya.

Saboda haka, muna jan hankalin 'yan uwa da abokai da cewa yanzu ne lokacin da muke da ƙarfin jiki da koshin lafiya ya kamata mu yi ƙoƙari wajen neman sana'ar da za ta ba mu tabbaci na dindindin.

Dole ne mu gane cewa aiki tukuru da gwagwarmaya wajen neman halal su ne za su gina rayuwa mai kyau, wacce za ta zama abin alfahari ga kanmu da kuma iyalanmu. Wannan shi ne mafita wajen tabbatar da cewa 'ya'yanmu za su taso cikin ingantacciyar rayuwa mai albarka da tabbaci.

Duk wanda ya rungumi sana'a da himma da niyyar neman halal, zai samu albarka da kwanciyar hankali cikin rayuwarsa. Sana'a ita ce ginshiƙin ci gaba mai ɗorewa, domin tana ba mutum tabbacin dogaro da kansa ba tare da ya zama wani nauyi ga al'umma ba.

Shawara ga 'Yan Uwa:

1. Mu rabu da dogaron aiki gwamnati ko siyasa kawai.

2. Mu koyar da kanmu sana'o'in hannu ko kasuwanci masu ɗorewa.

3. Mu ilmantar da kanmu da 'ya'yanmu kan muhimmancin dogaro da kai.

4. Mu dage wajen gudanar da rayuwa mai kyau, wacce za ta zama darasi ga waɗanda ke biyo baya.

Idan muka yi haka, za mu ga canjin rayuwa mai kyau, domin albarka na cikin neman halal. Wannan ne hanya mafi dacewa don tabbatar da makoma mai kyau.

Allah Ubangiji Ya kara daukaka da basira a rayuwanmu. Amin Ya Rabbi.

Mamuda Musa Kazaure
26/01/2025.

Ga cikakken bayani game da sabon Dokar haraji na TINUBU.Gwamnoni sun aminci da sabuwar dokar Haraji. Gwamnoni basu damu ...
17/01/2025

Ga cikakken bayani game da sabon Dokar haraji na TINUBU.

Gwamnoni sun aminci da sabuwar dokar Haraji. Gwamnoni basu damu da ko wani sashi na dokar ba, face Sharing Formulae, saboda shine zai taɓasu.

Toh yaya Sharing Formulae ɗin yake a da? Kuma yaya TINUBU yakeso ya maida shi? Sa'annan yaya aka amince dashi yau?

Yadda dokan yake ada:

Idan aka tara harajin ƙasa gaba ɗaya za'a raba shi kamar haka:

15% Federal Government
50% State Government
35% Local Government

Toh a rabon na jihohi ne dama ake rigimar. Ma'ana wannan 50% ɗin na jihohi a maida shi 100% a raba shi ga jihohin, inda a zamanin da ake raba:

- 50% Equality: Za'a raba dai-dai ga kowacce jiha. (37)
- 30% Population: Za'a based on population, kenan inda sufi yawa su zafi ɗiba a wannan kason
- 20% Derivation: A nan kuma ana rabawa ne, based on Abunda jiha ta bayar a cikin kuɗin harajin.

Amma zuwan TINUBU sai yace yanason a dinga raba, rabon jihohi kamar haka..

- 20% Equality (Dai-dai)
- 20% Population (Yawan jama'a)
- 60% Derivation (Abunda jiha ta bada)

To daga nan ne, Gwamnonin Arewa s**ace basu yarda ba, saboda idan akace 60% Derivation, toh tabbas bazasu samu komai ba saboda jihohinsu basa bada komai na haraji idan ka haɗa da Lagos, saboda jihar Lagos kaɗai ta shafe jihohin Arewa dukka, tama fisu. Kunga kusan 50% na kuɗin Jihohi zai je Lagos da Porthacourt kenan! Toh kunji dalilin dayasa s**aƙi amsa.

Amma yanzu sun dai-daita a wannan rabon.

- 50% Equality (Dai-dai)
- 20% Population (Yawan Jama'a)
- 30% Derivation (Kuɗin da jiha ta kawo).

Wannan shine wanda Gwamnoni s**a amince, amma dukda hakan kuɗin shiga na Lagos zai ƙaru, Saboda Derivation ya ƙaru da kashi 10%.

Jama'a menene ra'ayinku akan amincewar Gwamnonin nan? Hakan yana nuna TINUBU ya gagara kenan?

Mai fassara: Abubakar Gambo.

Congratulations Dr Nura!Jama'a barkanmu da warhaka. Ina murnan sanardaku cewa daya daga cikin gagga-gaggan mutane, wadan...
16/01/2025

Congratulations Dr Nura!
Jama'a barkanmu da warhaka. Ina murnan sanardaku cewa daya daga cikin gagga-gaggan mutane, wadanda s**a taka rawa wajen kafa kungiyar fafutukan ceton hakkin bil-adam ta CUPS, ya zama kwamishina a Jihar Kano.

Masha Allah, Alhamdulillah, a madadin dukkan al'ummanmu da ke cikin kungiyar CUPS, Dr Nura Iro Ma'aji, muna taya ka murna. Muna yi maka addu'a da fatan Alheri. Allah Ubangiji Ya kiyaye ka, Ya tsare ka. Allah Ubangiji Ya taya ka riko da hannunsa. Amin Ya Rabbi.

Tabbas, mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sa kwarya a gurbinta. Domin kuwa nada Dr Nura a matsayin Kwamishinan Bibiya da Tantance Ingancin Aiki ba karamin tasiri zai yiwa Jihar Kano ba.

Mu dai a CUPS mun san cewa masu gudu su gudu!

Na barku lafiya.

Dr Idris Ahmed.
CUPS.
16/1/2025.

30/12/2024

Nayi magana da General Tukur Gusau!

Jama'a barkanmu da warhaka. Yau da safe misalin karfe 9.00 AM, na sami daman yin chat da kakakin sojojin Najeriya, Brigadier General Tukur Gusau.

Na nuna masa yadda mu al'umman Arewa bamu ji dadin yadda ya fito fili ya zura karya akan kisan gilla wadda sojojin jiragen sama s**a yiwa al'ummanmu a Jihar Sokoto ba.

Tabbas, General ya wanke kansa, inda yayi bayanin cewa ai abinda ya fada ba ra'ayinsa bane, ra'ayin defence HQ ne!

Toh Jama'a, wani irin aiki ne wannan wadda za'a kashe mutane kisan gilla, ayi musu kage cewa su Lakurawa ne, sa'annan daga bisani kazo kana kare azzaluman da s**ayi kisan?

Me zaka gayawa Allah Ubangiji gobe ranan hisabi? Dole ne sai kayi irin wannan haramtaccen aikin? Kai malami ne, kuma kayi karatu har zuwa PhD a jama'ar Leicester dake nan Britannia. Zaka iya samun aiki a duk fadin duniyan nan. Allah Ka sa mudace. Amin.

Jama'a wannan shine karo na uku, wadda sojojin jiragen sama suke kashe mutanen Arewa ba tare da laifinsu ba. Gwamnatin Tarayyan Najeriya ta nuna halin ko oho, domin kashe dan Arewa kamar kashe kiyashi ne! Gwamnatin Tarayya bata nemi gafara ba, b***e ta biya diyyah!

Irin wannan tsananin zalunci da girman kai da wannan Gwamnatin Tarayyan Najeriya take nuna mana, ya zama wajibi a kanmu,, mu mutanen Arewa, mu dukufa mu shaidawa Allah Ubangiji halinda muke ciki. Al-Qunut itace kadai mafita!

Na barku lafiya.

Dr Idris Ahmed.
CUPS.
29/12/2024.

25/12/2024

Sanarwa daga CUPS!

Jama'a barkanmu da warhaka. Barkanmu da sake saduwa a wannan dandalin mai tarin Albarka.

Jama'a ku gafarcemu domin mun kwana biyu bamu baku update ba. Hakan Ya faru ne domin muna tsara shirye-shirye daban daban domin gudanarda harkokin CUPS a duk jihohin Arewa.

Muna da update kamar haka:

1. Muna ci gaba da hada database na Yan kungiyarmu ta CUPS. Har yanzu akwai mutane da kuma kungiyoyi masu sha'awan shiga kungiyar CUPS. Lissafi ya nuna mana cewa munada Yan kungiyarmu daga duk fadin Najeriya har ma zuwa kasashen waje.

2. A kungiyar CUPS muna da kwararru a fanni daban daban na rayuwan bil-adam. Akwai Dalibai, Malamai, Likitoci, Engineers, Yan Siyasa, Yan Kasuwa, Ma'aikatan Gwamnati, Jami'an Tsaro, da kuma Matan Aure.

3. Daga sunayen wadanda s**a yi ragista, muna da isassun kwararrun mutane, mata da maza, kuma matasa, wadanda zasuyi shugabancin Directorates (Directors), shugabancin Jihohi, da kuma shugabancin kananan hukumomi.

4. Nan ba da jimawa ba, zamu wallafa sunayen directors da kuma shugabannin Jihohi da na kananan hukumomi na wucin gadi. Zamu bawa kowace jiha dama ta zabi shugabanta da kuma shugabannin kananan hukumomi.

5. Domin kasancewa muna da isassun kwararru a duk fadin Arewa, akwai yiwuwan CUPS ta fara aiki lokaci guda, a duk fadin Jihohin Arewa, ba sai mun sami jinkiri ba.

6. Muna hada lissafin kamfanoni da kungiyoyi daban-dabam na cikin gida da na waje, wadanda kungiyar CUPS zata yi aiki dasu, domin cimma burinmu na ceton Arewa da al'ummanta daga halaka. Zamu wallafa sunayen wadannan kamfanoni da kungiyoyi nan gaba.

7. Idan Allah Ubangiji Ya yarda, muna da burin kafa ofishinmu a Jamhurriyar Nijar, Ghana, America, Germany, Russia, Malaysia da kuma China. Munada Yan Arewa da yawa a wadannan kasashen, wadanda muke kyakkyawan zato zasu taimakemu wajen ceton Arewa da al'ummanta daga halaka.

8. Zamu wallafa a duk kafofin sada zumunta na yanan gizo, sabon kundin tsarin mulkinmu na CUPS (Constitution). Wannan zai taimaka wajen ilmantarda Jama'a gida da waje, manufofin kungiyar CUPS.

Toh Allah Ubangiji Ya daafa mana akan wannan tafiya na ceton Arewa da al'ummanta. Amin Ya Rabbi.

Jama'a na barku lafiya.

Dr Idris Ahmed.
CUPS.
25/12/2024.

Jama'a barkanmu da warhaka. Tunda Allah Ubangiji Ya sa mun iso Kano lafiya, kuma mun sami masauki mai inganci daga maigi...
21/11/2024

Jama'a barkanmu da warhaka. Tunda Allah Ubangiji Ya sa mun iso Kano lafiya, kuma mun sami masauki mai inganci daga maigidanmu Professor Sir Aliyu A. Jibia, ayyukan matasa da zamu fara gudanarwa a Jihar Kano suna nan kamar haka:

1. Koyar da sana'an gyara computer/printer.
2. Koyar da sana'an gyara mobile phone.
3. Koyar da sana'an electrician.
4. Koyar da sana'an plumber.
5. Koyar da sana'an bricklayer.
6. Koyar da sana'an painter/POP
7. Koyar da sana'an carpenter.
8. Koyar da sana'an welder.
9. Koyar da sana'an solar panels.
10. Koyar da sana'an CCTV.
11. Koyar da sana'an dinki.
12. Koyar da sana'an kitso.
13. Koyar da ilimin computer da ICT.
14. Koyar da ilimin crypto.
15. Koyar da ilimin Artificial Intelligence.
16. Koyar da ilimin noma abinci a gida.
17. Koyar da ilimin kiwon kaji.
18. Koyar da ilimin kiwon kifi.

Duk matashi da muka dauka domin training, zamuyi masa training a kyauta ne. Kuma ko wani matashi za'a bashi jari mai tsoka, toh amma zai dawo da kudin, idan Allah Ya sa sana'arsa tayi Albarka. Zamu bukaci kudin domin wasu matasan suma su amfana.

Toh Jama'a, me zaku ce dangane da wannan tsarin? Wace sana'a ce kuke ganin matasa zasu fi bukata a Jihar Kano? Muna jiran shawarwarinku. Mungode.

Na barku lafiya.

Dr. Idris Ahmed.
CUPS.
21/11/2024.

16/11/2024

Sanarwa daga CUPS!

Jama'a, mun kammala taron kwamitin gudanarwa da safiyan yau. Mun amince da Manifesto/Master Plan na CUPS. Gabaɗaya, an kawo ra'ayoyi guda 30 don yin muhawara a kansu.

Ina mai farin cikin sanar da ku cewa za mu kafa ofishinmu na farko a Najeriya a birnin Kano. Sannan kuma wasu ofisoshi guda biyu, daya aa Kaduna daya kuma a Abuja. Amma daga bisani, zamu kafa ofishinmu a duk sauran Jihohin Arewa.

Nadin kwamitin gudanarwa na kwarai, rajistar zama memba da bayar da katin ID na biometric tare da fakitin maraba sune ayyuka mafi fifiko na gaba a cikin tafiyar mu. Muna da niyyar fara aiki wurjanjan ba tare da bata lokaci ba.

Jama'a muna godiya matuka da irin goyon baya da kuke bamu. Applications na zama membobin CUPS da muka samu sun wuce yadda mukayi hasashe nesa ba kusa ba.

Allah ya saka muku da alkhairi. Amin.

Dr. Idris Ahmed.
CUPS.
16/11/2024.

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when KANO STATE FORUM posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category