30/10/2024
Tun bayan samun Yan'cin Kai aka fara kashe su Sardauna wai da zargin rashin iya mulki da cin kudin Kasa. Daga wannan ya hau wannan ya kwace yace Bai iya ba, har akayi zabe lokacin Shagari a 1979-1983, Sannan akace Bai iya ba, soja yakarba.
Haka akayita dagulawa har zuwa 1999, aka sake komawa zuwa Dimokaradiyya zuwa yau, duk wadda ya hau ace gara jiya. Andai gagara samun wadda yayi fice.
Mutane sunata kiraye-kirayen cewa gara ma mulkin Soja akan wannan Dimokaradiyyar, saidai fa abinda Kuma aka manta shine, yanzu ne mutane sukeda yan'ci na zaben wadda suke so, sannan idan ma sun zaba Bai musu abinda yadace ba su chanja, sabanin wanchan lokacin.
Kawai abinda ake bukata a wannan zamanin shine, cire son zuciya, Sanin Yan'cin Kai dakuma son cigaban Kasa agun kowa ba tareda mumafurci ba. Ta haka ne za a iya dauko hanya gyara, sauran Kuma Abarwa Mai kowa Mai komai.