Tijjani yusuf guruntum

Tijjani yusuf guruntum sunnah makamin mumini���

18/10/2025

Allah ya taimaki Malam ya saka maka da Alkhairi 🤝🤝 sunnah gidan hujjoji 🙌🙏🙏

❝Duk Abin Da Zaka Nema Arayuwar Duniya Ka Kiyayi Dukiyar Haram❞Sheikh  Mallam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum  Hafizahullah
18/10/2025

❝Duk Abin Da Zaka Nema Arayuwar Duniya Ka Kiyayi Dukiyar Haram❞

Sheikh Mallam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum Hafizahullah

SHEIK GURUNTUM: Kodai Shine Magajin Sheik Ja'afar Ta Fuskar Iya Sarrafa Harshe?Daga Abubakar Shehu DokokiIdan Allah Ya y...
02/10/2025

SHEIK GURUNTUM: Kodai Shine Magajin Sheik Ja'afar Ta Fuskar Iya Sarrafa Harshe?

Daga Abubakar Shehu Dokoki

Idan Allah Ya yi maka baiwa ka gode masa, sai kuma Allah Yabƙara maka, ɗaya daga cikin ni'imar da Allah Ya yiwa arewa a yanzu akwai manyan malamai masu gogayya da manyan malaman duniya, a cikin masu baiwar aika saƙo cikin hikima da misali abin burgewa akwai Mallam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum.

Tabbas mun yi kewar manyan malamai irin su Sheik Ja'afar, Albani, Sheik Bamba da sauransu, amma babbar baiwar da Allah Ya yi Sheik Ja'afar akwai iya sarrafa harshe, wanda a yanzu babu wanda yake kwatanta sarrafa harshen Hausa da lafazi mai sauƙin ganewa irin Sheik Guruntum.

Ana yi wa Malam Guruntum laƙabi da 'Likitan Zuciya' ko kuma ka ji ana cewa injiniyan gyaran zuciya, shine Malamin da za ka riƙa jin karatunsa amma har baka so a zo ƙarshe.

Akwai wani misali da Malam ya bayar cikin wani karatu, inda Malam ya ce "Man Sagir, Daga Sanda Mutum Ya Shekara Arba'in, Hamsin ko Sittin, Lahira Ko A Ƙasa Ake Zuwa Ai Ya Kusa Kai Wa ."

Wannan misali ne wanda kowanne irin mutum zai gane, kuma dole zai girgiza shi (komai ƙarancin fahimtar mutum).

Muna addu'ar Allah Ya ƙarawa Malam lafiya da nisan kwana.

Ko za ka iya tuna wani misali da Malam Ya bayar?

Address

Bauch
Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tijjani yusuf guruntum posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category