01/04/2026
KEMA KINA IRIN WANNAN HALAYYAR IDAN KINA HAILA KO KUWA?
Wasu mata da yawa suna sakaci. Da ibada lokacin da suke haila. Wllh wasu kaace sun bar musulunci ne idan suna haila. Wa,iya zubillahi, to mata kusani. Haila bata hana ibada. Abunda ya tabbata A' Shari,a , Mai haila take bari. Acikin ibada shine. Azumi da sallah , Azumi shi zata rama idan tayi tsarki. Sallah kuma wannan base ta rama ba, wata zatace to karatun ALQUR "ANI,FA? Shi karatun Al, Qur'Ani, malamai sunyi maganganu akanshi, jamhur na malamai sun tafi akan mace mai haila zata iya daukan wani sashi na Al Qur'Ani. Ta karan ta. An tambayi wani daga cikin magabata. Akace masa mace Mai haila zata iya karanta Al, Qur'Ani, acikin wayar ta,? Yace wannan babu laifi,. Zata iya.
Amma me yasa mata wasu daga cikinsu idan suna haila. Za kaga sun fita daga cikin rayuwar musulunci? To gsky wannan kuskure ne Sosai, kuma laifi ne, domun ba,a, hanaki AZKAR ba na safe da yanmaba. Ba,a, hanaki ki tashi gabda fitowar alfijir. Ki roki Allah ba kuma kiyi istigifari, domun ita kanta ADDU,AN ibada ce AZKAR , shima ibada ne, da sauran maka mantan wannan. To don Allah mata mu gyara wannan dabi,ar. Karki mutu ki hadu da Allah. Kina barin ibadun daba,a haramta maki ba idan kina haila, kuma yana daga cikin rashin wa,yau. Kiga mace ance ta bar sallah, tabar azumi, me makon wannan lokacin da aka bata, ta samu ta cikeshesu, da wasu ibadun, Amma kuma ake sakaci dasu, mu duba rayuwar matan (Annabi Muhammad. S,A,W, ba haka suke ba,. Mu duba rayuwar matan sahabbai. Suma ba haka suke ba,. To me yasa mu matan mu wasu daga cikinsu suke sakaci da hakan? Gaskiya wannan ba ,halin mumina bace. Shifa mumini. Idan wata ibada ta kubuce masa, bayan damuwa da zaiyi. Se kaga yana neman wata hanya. Da zai cike wancen Ibadan data kubuce masa,. To haka mumini yake. Don Allah yan uwa mata agyara wannan dabi,ar
Allah ubangiji ya bamu iKon gyarawa, ya sanya mu cikin. Ibadurrahman,. Amin
( naja'At Abbkr. Ummu taufeq ✍️✍️).
M,N