24/08/2022
IYAYE BAYAN SUN MUTU
Wani bawan Allah yana zaune kusa da abokinsa sai yaga yana raba yadda zai kashe kudin albashinsa na wata:
Yasa N20,000 ga abincin gidansa.
Yasa N3,000 ga Bills.
Yasa N2,000 ga madarar yara.
Yasa N2,000 ga hidimar Mahaifiyarsa.
Yasa N2,000 ga Mahaifinshi.
Sai abokin yace masa a'a, ba Iyayenka sun rasu da daÉ—ewa ba?
Sai yace eh sun rasu, amma suna RAYE a ZUCIYATA! Bazan MANTA da su ba. Yanzu ne s**a fi BUKATAR in yi kasafi (BUDGET) da su don ba zasu iya yiwa kansu komai ba bayan mutuwa sai abin da nayi musu na kyauta da SADAKA.
Allahu Akbar!
Mu sani har yanzu suna da HAKKI a kanmu.
Mu dage da yi musu sadaka da kyauta don nema musu gafara a wurin Mahalincinmu, Ubangiji Allah (SWT).