Sheikh Abduljabbar Supporters

Sheikh Abduljabbar Supporters Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sheikh Abduljabbar Supporters, Kano.

Wannan page mun qirqire shi ne bisa shawarwarin yan uwa da su ke ba mu na bude wani group ko page da zai dinga kawo abubuwan da s**a shafi Ameeril Wa'izina Sheikh Dr. Abduljabbar Sheikh Dr. Nasiru Kabara

09/08/2025

Salamu alaikum!
Yan uwa Musulmi baki daya Muna yi mu ku fatan Alkhairi.
A tsakanin jiya na ga wani rubutu da da ni mutum Jilani Makwarari ya kawo wani rubutu da Wai cewa wai Yan Shi'a na cutar da Shaikh Abduljabbar har ya fara rubutu a kan haka!
Na Yi mamaki ta wata fuskar ban Kuma Yi mamaki ba ta wata fuskar.
Ina son shi Jilani Makwarari da masu tunani irin nasa su sani, Yan Shi'a ba su damu da jingina kansu ga kowa ba sai dai Neman hadin kan Musulmi domin ci gaban Musulunci.
Shaikh Abduljabbar yayi kokari matuqa wurin shiryatar da mutane son Ahlulbayt (a.s) da Kuma cirewa wadansu qiyayyar Shi'a ba ma musu a kan haka.
Wannan page da group na Shaikh Abduljabbar Supporters ni ne na bude shi a lokacin da aka k**a Shaikh Abduljabbar Kuma da yawan mabiyan Shaikh Abduljabbar s**a tsorata s**a Daina rubutu wadansu daga cikin Manyan marubutan s**a dinga cewa: An kwace musu account!
Ana wannan dambarwar ne na Yi nazarin me zan iya yi sai na bude wannan page da Kuma group domin zaburantarwa ga Yan uwanmu Yan Ashabul Kahfi.
Ni Dan Shi'a ne mabiyin Sayyid Ibraheem Zakzaky (h) Kuma har gobe Ina nan a kan bakana, ana zaluntar Shaikh Abduljabbar Kuma zan ci gaba da bayyana an zalunce shi.
Imam Ali (a s) yana cewa: "Ku zama masu Husuma ga Azzalumai sannan masu taimakon Wanda aka zalunta."
Ina son masu son tada wannan fitinar su sani lallai Gwamnati na iya shirya wannan makircin domin Raba kawunanmu su ci gaba da zaluncinsu. Suna da wani Abu da bature ke cewa: "Divide and rule". wato raba ka mulka, suna Raba kawunanmu ne domin su ci gaba da zaluntarmu.
Dukkanin bangarorin shi'ar da Ashabul Kahfi duk zaluntarmu ake yi.
Kuma kun shaida zaluncin kusa-kusan Nan da Buhari ya kaddamar a Zaria a shekarar 2015 a Dec. Yadda aka kashe mutane sama da dubu da lalata wuraren Ibada!
lokacin wannan Zaluncin na Buhari Yan Ashabul Kahfi ba su gujemu ba!
Ku guji rarraba domin ba ta kawo komai sai cutarwa!

26/06/2025

Ire-iren wadannan hadisan Shaikh Dr. Abduljabbar Shaikh Dr. Nasiru Kabara ya ke korewa!
Nan Lawan Triumph ne ke kokarin tabbatar da hadisan wani Malami ke haskawa

السلام عليكم ورحمة الله وبركاته. إياك نعبد وإياك نستعين.07-02-2024.________________SANARWA!!!Daga Dan uwan ku ABDULJABBA...
07/02/2024

السلام عليكم ورحمة الله وبركاته.
إياك نعبد وإياك نستعين.
07-02-2024.
________________
SANARWA!!!

Daga Dan uwan ku ABDULJABBAR SHEIKH NASIRU KABARA!!!

Game da sabon appeal wanda na sami labarin (wasu mutane sun shigar da shi da sunan (WAI) Dalibai na ne su, ina sanar da Duniya cewa, wadannan mutane basa tare da Ni a wannan rintsi, wadannan mutane suna aiki ne tukuru tare da Azzaluman da s**a shirya min wannan ta'addanci, suna aiki ne ka'in da na'in wajen ganin sun tabbatar da wannan kage da GWAMNATI ta yi min, wadannan mutane yaran ADAMU ADAMU ne, ma'ana wannan sabon appeal da aka sa su s**a shigar shine lalata appeal din da na shigar tun a ranar 23-12-2022, masu zalutata sun dau wadannan mataki ne sak**akon gazawarsu a shari'ar da ta gabata a KOFAR KUDU da rusbawar su a kakaba min lefin yin BATANCI GA MA'AIKIN ALLAH (SAWAW) da tabbacin da suke da shi ne idan har aka bar hujjojina s**a shiga cikin appale ba makawa High Court zata rushe ilahirin da ta gudana a U S C K K zata wanke Ni daga wannan kage da s**a yimin, wannan yasa s**a dau matakai guda biyu k**ar haka:-

1 - Rusa appeal din da na shigar tun ranar 23-12-2022.
2 - Kakaba min sababbin lefika a karkashin SECTION (275 & 375).

Masu zalunta ta sun dau wadannan matakai cikin rufewar ido tare da cewa kowa ya san shari'ar da ta gudana a U S C K K ta gudana ne a kan SECTION (382) K S S P C L 2000 shi kadai. wannan shine hadafin su na shigar da wannan sabon appeal a hankali yanzu.
___________________________
Sako na izuwa ga wadannan Azzalumai:-
الَّذِينَ قالَ لَهُمُ النَّاسُ إِنَّ النَّاسَ قَدْ جَمَعُوا لَكُمْ فَاخْشَوْهُمْ فَزادَهُمْ إِيماناً وَقالُوا حَسْبُنَا اللَّهُ وَنِعْمَ الْوَكِيلُ {♤} فَانْقَلَبُوا بِنِعْمَةٍ مِنَ اللَّهِ وَفَضْلٍ لَمْ يَمْسَسْهُمْ سُوءٌ وَاتَّبَعُوا رِضْوانَ اللَّهِ وَاللَّهُ ذُو فَضْلٍ عَظِيمٍ {♤}.
إِنَّمَا ذَلِكُمُ الشَّيْطَانُ يُخَوِّفُ أَوْلِيَاءهُ فَلاَ تَخَافُوهُمْ وَخَافُونِ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِين {♤} (صدقوالله العظيم).

Dan uwan ku Abduljabbar Sheikh Nasir Kabara (R).
عبد الجبار كبر
07-02-2024.

26/09/2023

Shawarwari garemu Yan Ashabul Kahfi daga rubutun Adam Abumajid Abu Baqara:
YAKAMATA DAN AS'HABUL KAHFI YASAN.....

duk wani yaqi an Gama yi masa shi, sannan duk wata dabara an rubuta masa an a jiye , na shi kawai ya dauko ya bibiya daga tarihi hanyar da aka bi aka yi Nasara ya sabunta ta sannan ya dauka, wacce aka yi kuskure a waccan tafiyar shi kuma ya gyara a cikin ta shi tafiyar,

Yak**ata mu Dan yi duba izuwa wasu Qarinoni da s**a faru Akan idanun duk wani Dan ashabul kahfi in dai ba qasa da shekaru 16 yake ba a halin yanzu da nake yin wannan Maganar!

A kwai wasu aiyukan Alheri da sheikh Abduljabbar (h) ya assasa su bai k**ata ace sun tsaya ba domin baya nan! , duk da Rawiyoyi da halqoqi sun yi qoqari wajen raya zikirin riyadul jannah kuma yanayin Armashi , Amma da zasu za6i wata rana guda daya su shirya taron zikirin na qasa a madadin taron khatama da shi sheikh Abdallah din ya assasa da sun Girgiza teburin... NUFUZIN su ya ci gaba da Qaruwa kuma abokan Gabar su zasu kasa bacci k**ar yadda s**a hana muku bacci , k**ar yadda yan uwa almajiran sheikh mazloom Ibrahim Yaaqoub El zakzaky (h) s**a ci gaba da raya tattaki na yaumul arba'in, duk da wanda suke zuwa wajen sa domin jaddada bai'ar su gare shi bayanan wannan ma ba umarnin sa ba ne daga baya umarnin shi yazo,,

Be k**ata irin kyaututtukan da sheikh Abduljabbar ya saba yiwa masu raunin cikin almajiran sa ta tsaya bayan baya nan ba, k**ar yadda almajiran sheikh El zakzaky s**a ci gaba da Rabon kayan abinci ga wadanda shehun malamin yake yiwa wasu al'ummar tun kafin akai ga zalintar sa,,

Shi fa ku gane wannan,!! yan uwa yan ashabul kahfi, Kiran wadannan bayin Allahn ba wai kira ne na yin fito na fito da shugabanni ba! A'a kira ne da yin fito na fito da zalinci, duk wanda Ka gani yana matsayin shugaba Amma yana kallon wadannan shehunan malaman a matsayin barazana! believe me! Azzalumi ne, Da baya zalinci babu Abinda zai saka shi ya tsargu! Me yasa adalan shuwagabannin basu da irin wannan barazanar? Fitowa domin yin tattaki na lumana ba yana nufin Kun fito ku ja layi da shugabanni ba ne, A'ah illa iyaka zaku tunawa shugabanni ne cewa Ana zalintar ku, kuma Alhali kuu ma yan qasa ne k**ar kowa! , Ina son muridai su San wannan,

sannan ba ko yaushe ne ake jiran umarnin jagora ba kafin aiwatar da Abinda yake daidai ne ko wanda ya dace , a 6angaren yan uwa almajiran Malam (h) FIKIRAR Abuja struggle ba umarnin Malam aka jira ba lokacin da aka soma wannan sabuwar gwagwarmayar, kuma Babu shawarar sa domin lokacin da aka fare ta babu wanda ma yasan inda shehun malamin yake cikin almajiran shi, ga shi kuma kwalliya ta biya kudin sabulu,

Sannan k**ar ita kan ta harkar tsaron jagora ba'a buqatar umarnin shi a wasu lokuta domin a ba shi kariya, saboda shine ( risalar) gaba dayan ta, Idan an kashe shi to k**ar an qone muku littafin risalar ku ne wanda kuma shine kadai ya mallake shi,

Jagora k**ar birni ne masu tsaron shi kuma sune ganuwar birnin , babu hikima cikin tunanin Ka bawa jagoran Ka ran Ka! dai dai yake da an karya ganuwar wancan Garin Don haka sai Abinda birnin ya gani daga wulaqancin abokan gaba!

Shi jagora kana hana kan Ka mutuwa ne Ka kuma yi duk yadda zaka iya domin ba shi kariya Ka hana me cutarwa isa gare shi, ina dabara ga wanda yake da damar tsira tare da jagoran shi Amma kuma Ka tsaya mutu su Ka isa gare jagoran na ka? , Idan abokan gaba sun taso ku gaba a filin yaqi burin su Idan sun kashe jagoran ku to sun karya ku, anan shi jagora zai fada muku ne ku tsaya kuyi Shahada saboda shi yana da total submission ne zuwa ga Allah, aljannah kawai yake kallo a wannan lokacin, , Amma ku masu tsaron sa Kun San cewa rayuwar sa muhimmiya a gare ku, Idan Kun rasa shi Kun rasa komai bayan ku zata 6al6alce, Don haka yanzu dauke shi ku 6oye shine wajibi a kan ku koda kuwa shi bai amince muku da yin hakan ba! Shaikh Nasrallah shine shugaban muqawamar da yafi kowa dadewa a raye domin sirrin hakan shine ya bar Jami'an tsaron shi suyi duk kan Abinda ya dace su yi domin kare shi,

Yaushe ne masu mumbari Akan social media na ashabul kahfi s**a ta6a shiryawa kan su taro gaba dayan su s**a halarta domin tuntu6ar juna,?

Ina aka kwana? Meye motsin mu na gaba? Wataqila suna yi Amma a daidaikun su, shima wannan yak**ata Su dauki darasi daga taron mu'utamar da almajiran sheikh El zakzaky suke shiryawa junan su lokaci zuwa lokaci kuma ko meye ke gaban mutum na uzuri s**an bari suje su halarci taron domin muhimmancin sa, wannan ya sanya hatta bayan malamin yana hannun azzalumai ku Ka GA memakon abin Yayi baya sai ma almajiran shi s**a sake samun sabon yaqini,

ba da addu'ah kadai s**a yi galaba ba, sai da s**a hada da sa'ayi tare da amfani da gwagwarmaya irin wacce azzalumi yake yi musu amfani da ita, BARAZANA su ba sa tsoron ta! KISA ba sabon Abu bane a gare su, su din tamkar FALASDINAWA NE A YAYIN INTIFADA! ku tuna cewa sheikh Abduljabbar ya ta6a yi muku wani karatu na BIDANATAINI ya kuma fada muku cewa duk kan annabi yana tare da su, da masu ba shi shawara ta gari, da masu ba shi shawara ta sharri, masharrantan cikin na shi sune masu amfanuwa da tsare shi da hukumomi suke yi, ku lura da wannan!

Bana wakiltar yan uwa almajiran Malam zakzaky (h) a wajen rubutu, haka kuma bana wakiltar yan'uwa almajiran sheikh Abduljabbar (h) a rubutu, abinda zai amfane ku cikin Abinda na fada ku dauka kuskuren ciki ku taya ni roqar Allah ya yafe mini bidi'o'in ciki ku bar mini Ka yana, fahintar shehu Timothy ce haka!

Saƙo na musamman ga dukkan yan makaranta da masoyan Maulana Dr  Sheikh Abduljabbar (Amirul wa'izina)--------------Assala...
01/09/2023

Saƙo na musamman ga dukkan yan makaranta da masoyan Maulana Dr Sheikh Abduljabbar (Amirul wa'izina)
--------------

Assalamu Alaikum

Tare da dukkan girmamawa da jinjina gare ku bisa juriya da jajircewar ku kan lamarin wannan jagora, ma'abucin sadaukarwa cikin hidima da bada kariya ga Annabi Muhammadu (s.a.w).

Zuwa yau cikin wannan wakiar da ta kwashe sama da shekaru biyu cikin bakin zalunci na sauya zance ga wannan bawan Allah mai kokarin bada kariya ga janabin ma'aikin Allah Annabin Rahama.

Kira ne na musamman kan dukkan ýan makaranta da masoya na gaskiya kan wannan tafiya, game da da-ga da gwagwarmayar da muke da gungun magauta makullata cikin lamarin wannan tafiya na hakikanin masoya Annabi Muhammadu (s.a.w) AS-HABUL KAHFI karkashin jagorancin Dr Sheik Abduljabbar Shekh Nasiru kabara (H).

A matsayin amanan tarayya don sauke nauyin da ya rataya a wuyan mu wajen ganin mun bada hakikanin gudunmawar da ta dace a wannan gaba kuma a wannan lokaci mawuyaci.

Hakan ne ya sanya mu yin kira na musamman ga dukkan yan uwa masoya don a sanya nafaha (gudunmawa) ga dukkan mai halin yin.

A yi tarayya da mu wajen sanya nafahar a asusun makaranta na mujamma'u ashabil kahfi warraqeem, k**ar haka.

Account number:
1140109791

Bank:
Polaris bank.

Name:
Assahabul kahfi warraqim Development Association.

Ana sanar da duk wanda ya ji ko ya gani cikin wannan zirin na masoya ya sanar da wanda bai ji ba cewar wannan nafaha ba'a dauke wa kowa ba duk yanda ya ke a fadin duniya matukar yana da hali.

Ga duk wanda ya samu daman sawa ya tura rasitin sa zuwa ga akwatin sako na shafin makaranta.

Allah ya sanya mu cikin ladan ibadan baki daya.

sanarwa📢
Majmu'at Atba'is Sheikh Abduljabbar Kabara (MASAK).
01/09/2023.

26/08/2023

Ba ma'ana za ka nuna mana ba, lafazi za ka nuna mana jahilai a gaban Shaikh Dr. Abduljabbar Shaikh Nasiru Kabara.

06/07/2023

Muna taya Yan uwa muminai barka da babban idi na Ghadir Khum!
Gobe ce Ranar Ghadir.
Muna godiya ga Allah ta'ala da ya Sanya mu masu riqo da wannan wilaya!

21/06/2023

Inna Lillahi wa inna ilaihi Raji'un.
Allah ya yiwa Malam Umaru Mai jakan karatu Rasuwa Babban Muqaddamin Qadiriyya a Limancin kona Zaria a yau Laraba Za'ayi Janazar sa karfe 5:00pm Anan Limancin kona, Munyi babban Rashi, kafin A maida irinsa aikine.
-yaɗa ilmi
- zumunci
-Shata halkar zikirullahi
-kyauta
-Gudun Duniya.
رحمك الله شيخ عمر مب جكر كرات رحمة واسعة وجعل قبرك روضة من رياض الجنة.

Dayyib Mustapha Muhammad Limancin kona Zaria.
21/6/2023

Allah Yajiƙan Malam yasa yahuta,

19/06/2023

Labbaika Sadauki!

03/06/2023

Alhakin Shaikh Abduljabbar Sai K**a su ya ke yi daya bayan daya!

07/05/2023

Yau ga irinta, an riƙe Liman, kuma lokaci na Sallah yayi.

Abban Malam a waƙar da ya yi wa Shaikh Sadauki (h).

Address

Kano

Telephone

+2347042025735

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sheikh Abduljabbar Supporters posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Sheikh Abduljabbar Supporters:

Share