Sheikh IDRIS zakariyya ya u yakubu

Sheikh IDRIS zakariyya ya u yakubu Wa Azantarwa nishadantarwa ilimantarwa fadakarwa

14/11/2024
Fadar shugaban kasa ta yi karin haske kan raɗe-raɗin da ke yawo cewa Tinubu ne ministan man fetur - Karanta a sashen sha...
28/10/2024

Fadar shugaban kasa ta yi karin haske kan raɗe-raɗin da ke yawo cewa Tinubu ne ministan man fetur - Karanta a sashen sharhi.

Ga wata babbar damar dogaro da kai ga matasa daga gwamnatin tarayya. Ina matasan Najeriya! Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed ...
28/10/2024

Ga wata babbar damar dogaro da kai ga matasa daga gwamnatin tarayya.

Ina matasan Najeriya! Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ƙaddamar da sabon Shirin ta mai taken “Renewed Hope Employment Initiative”. Wannan shirin zai samar da aikin yi da koyar da sana’o’i ga matasa 93,731 a faɗin Najeriya. Bugu da ƙari, zai bada jari na fara sana’o’in ga waɗanda s**a samu horon, sannan kuma za a baiwa wasu damar samun lamuni dan gudanar da ƙananu da matsakaitan kasuwanci.

Shirin na daga matakin da Gwamnatin ke ɗauka don wadata ƴan Najeriya da aikin yi, ƙarfafa dogaro da kai da kuma bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar.

Masu buƙata zasu iya shiga adreshin yanar gizo ta intanet kamar haka;

www.nde.gov.ng

Abubuwan da ake buƙata domin yin rejista; Asusun Email, hoton fasfo, nambar shedar ɗan ƙasa NIN.

Za a tuntubi waɗanda aka zaba kai tsaye ta kan adreshin Email din da s**ai rejista da shi. Sannan kuma akwai alawus da za a baiwa dukkan waɗanda za a baiwa horon a faɗin ƙasar nan.

An fara rejista a ranar Litinin, 21 ga watan Oktoba, 2023, za kuma a rufe a ranar Talata 31 ga watan Disamba, 2024.

Kada ku bari ayi babu ku.

Yadda wani fasihin matashi a jihar Kano ya kirkira keke mai kafa uku dake amfani da hasken rana maimakon man fetur..
28/10/2024

Yadda wani fasihin matashi a jihar Kano ya kirkira keke mai kafa uku dake amfani da hasken rana maimakon man fetur..

Jamhuriyyar Musulunci Ir@n ta kammala shirye shiryen maida martani ga kasar Isr@'il@ biyo bayan ha*rin wasan kwaikwayo d...
26/10/2024

Jamhuriyyar Musulunci Ir@n ta kammala shirye shiryen maida martani ga kasar Isr@'il@ biyo bayan ha*rin wasan kwaikwayo da kasar ta Isr@'il@ ta kai a Jiya.

Cikin kasashen biyu wa kuke wa fatan nasara?
Daga Idris ya u Yakubu

Yanzu-yanzu: Tinubu ya sauya Betta EduShugaba Bola Tinubu ya sauya Betta Edu, tsohuwar ministar harkokin jin kai da rage...
24/10/2024

Yanzu-yanzu: Tinubu ya sauya Betta Edu

Shugaba Bola Tinubu ya sauya Betta Edu, tsohuwar ministar harkokin jin kai da rage talauci, da Dr. Nentawe Yilwatda.

A watan Janairu, Tinubu ya dakatar da Edu bayan ta bada umarnin tura Naira miliyan 585.2 zuwa asusun banki na sirri na wani ma’aikacin gwamnati, wanda ke matsayin akawu mai kula da tallafin marasa ƙarfi a Najeriya.

Shugaban ƙasa ya kuma nemi hukumar EFCC ta gudanar da cikakken bincike kan duk wata mu'amala ta kuɗi da wannan ma'aikata ta gudanar.

Binciken ya faɗaɗa har zuwa tsarin ayyukan tallafin jama’a na Najeriya.

Edu ta musanta yin wani laifi.

Ofishinta ya bayyana a wancan lokaci cewa ta amince da tura kuɗin zuwa asusun sirri domin “aiwatar da shirin bayar da tallafi ga marasa ƙarfi.”

Ofishin Akanta Janar na Tarayya ya ce irin waɗannan kuɗaɗen yakamata su tafi kai tsaye daga asusun gwamnati zuwa ga masu amfana da tallafin ba zuwa asusun wasu tsirarun mutane ba.daga idris ya u Yakubu

Na Yafewa Wadanda S**a Kwashi Man Fetur A Yayin Da Tanka Ta Fashe A Garin Majia Jihar Jigawa Saboda Wadanda S**a Rasu Su...
24/10/2024

Na Yafewa Wadanda S**a Kwashi Man Fetur A Yayin Da Tanka Ta Fashe A Garin Majia Jihar Jigawa Saboda Wadanda S**a Rasu Su Samu Salama A Kabari, Su Kuma Wadanda S**a Samu Rauni Allah Ya Ba Su Lafiya, Inji Mamallakin Man Fetur Din

Me za ku ce?

Zan kori masu Barace Barace a birnin Tarayya Abuja - Wike._________Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike, y...
24/10/2024

Zan kori masu Barace Barace a birnin Tarayya Abuja - Wike.
_________

Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike, ya shelanta yaki da barace-barace da yace hakan yana lalata birnin Abujan, tare da haifar da matsalar tsaro.

Wike ya bayyana hakan ne a lokacin da aka ƙaddamar da fara aikin titin hanyar da ta tashi daga Nnamdi Azikiwe Expressway zuwa Judges Quarters, a gundumar Katampe, Abuja a jiya Talata.

Ministan ya ce daukar matakin ya zama dole saboda fargabar cewa Abuja na rikidewa zuwa garin almajirai. A halin yanzu.

“Bari na fadi a fili yanzu, mun shelanta yaki da mabarata saboda Abuja na neman komawa birnin mabarata.

“Idan ka san kana da ‘yar uwa, kana da dan’uwa da ke yawon bara a hanya, ka yi wani abu, domin daga mako mai zuwa, za mu dauke su; za mu fitar da su daga cikin birni.

“Abin kunya ne a ce mutanen da suke kawo ziyara Abuja, abin da s**a fara gani kawai mabarata ne a kan Titin Abuja wannan ba zai yuyu ba ” inji shi. Minista Wike.

Me zaku ce kan hakan?

Da dumi-dumi: Shugaba Tinubu ya kori ministoci biyar.1. Barr. Uju-Ken Ohanenye, Ministan Harkokin Mata2. Lola Ade-John, ...
24/10/2024

Da dumi-dumi: Shugaba Tinubu ya kori ministoci biyar.

1. Barr. Uju-Ken Ohanenye, Ministan Harkokin Mata

2. Lola Ade-John, Ministan Yawon Bude Ido

3. Farfesa Tahir Mamman, Ministan Ilimi

4. Abdullahi Muhammad Gwarzo, Ministan Jiha, Gidaje da Raya Birane

5. Dr. Jamila Bio Ibrahim, Ministan Raya Matasa.
Daga idris ya u Yakubu

Mutanen Da S**a Mutu A Wajen Tankin Man Fetur A Jigawa Sata S**a Je Yi, Domin Ba Man Su Ba Ne, Don Allah Iyaye Mu Tarbiy...
24/10/2024

Mutanen Da S**a Mutu A Wajen Tankin Man Fetur A Jigawa Sata S**a Je Yi, Domin Ba Man Su Ba Ne, Don Allah Iyaye Mu Tarbiyartar Da 'Ya'yanmu Domin Sanin Bambancin Halal Da Haram, Inji Sheik Idris Dutsen Tanshi

Me za ku ce?

Daga idris ya u Yakubu

ABIN SHA'AWA: Ɗan Wasan Ƙungiyar ƙwallon ƙafa  Ta Shakhtar Kenan "Alaa Ghram"  Lokacin Dayake Karatun Alkur'ani Mai Tsàr...
24/10/2024

ABIN SHA'AWA: Ɗan Wasan Ƙungiyar ƙwallon ƙafa Ta Shakhtar Kenan "Alaa Ghram" Lokacin Dayake Karatun Alkur'ani Mai Tsàrki, awanni kaɗan kafin Fara Wasansu A satin Daya Gabata.

Daga idris ya u Yakubu

Address

Gezawa
Kano

Telephone

+2349132743939

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sheikh IDRIS zakariyya ya u yakubu posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category