Muryar masu rauni

Muryar masu rauni Mun bude wannan shafin neh domin bayyana zaluncin azzalumai da kuma kira ga kungiyoyin neman yanci da su tashi tsaye domin kare raunana

SHAHADAR NSRH TA GADAR DA JURIYA KAN GWAGWARMAYA GA MASU ‘YANCI,-Bin Muhammad 2025-10-01 H.TVShekara guda bayan shahadar...
06/10/2025

SHAHADAR NSRH TA GADAR DA JURIYA KAN GWAGWARMAYA GA MASU ‘YANCI,

-Bin Muhammad
2025-10-01 H.TV

Shekara guda bayan shahadar Sayyed Hassan mai nasara, yanayin siyasa da zamantakewar yankin ya sake yin tasiri da tunawa da shi. Nan da nan kuma shahadarsa ta zama wani muhimmin batu na samun hadin kai a tsakanin kungiyoyi masu adawa da mamaya da kuma sabunta himma ga manufofin tsayin daka.

Sayyid Hassan Nasrallah, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya yi shahada a ranar Juma’a 27 ga watan Satumba, 2024, a wani hari da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta kai a yankin Dahiyeh da ke kudancin birnin Beirut.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Pars Today cewa, Shahid Hasan Nasrallah ya jagoranci kungiyar Hizbullah tun a farkon shekarun 1990, kuma ya shafe sama da shekaru 30 yana da tasiri a ci gaban kasar Labanon da kuma yankin. Ya yi nasarar sauya kungiyar Hizbullah daga kungiyar gwagwarmaya ta cikin gida zuwa wani babban jigo a harkokin yammacin Asiya. Halinsa na kwarjini, gaskiyarsa wajen bayyana matsayi, da iya tafiyar da rikice-rikice masu rikitarwa na daga cikin muhimman halayensa.

Daidai matsayinsa na dabara ne ya sa aka kashe shi a harin da ba a taba ganin irinsa ba a shekarar da ta gabata a watan Oktoba ya dauki hankalin al’ummar duniya. Amma duk da haka shahadar Nasrallah ba ita ce karshen tafarkinsa ba. Jim kadan bayan sanar da shahadarsa, fushi da bakin ciki sun mamaye kasar Labanon da ma duniyar musulmi. Al’ummar kasar Labanon sun karrama shi a bukukuwa daban-daban, kuma an sake tada hotunansa a titunan birnin Beirut da garuruwan kudancin kasar.

A Iran da ma sauran kasashen yankin, an kuma gudanar da bukukuwan tunawa da su, inda masu jawabi s**a jaddada ci gaba da tafarkin tsayin daka. Muzaharar jana’izar da aka gudanar bayan watanni da dama, ta rikide zuwa gagarumin nunin hadin kan kasa da kasa. Kasancewar mutane tare da masu siyasa da addini sun nuna cewa farin jinin Nasra

03/10/2025

*KU KARANTA ZA KU AMFANA*

*HIRA DA JAWAD ƊAN SAYYID HASSAN NA*SRULLAH* Cikin hirar nan akwai darasi babba, wajen da ya fi burgeni shin ne Sayyid na karɓar ƘALUBALE da GYARA

Almayadeen; me kafi so dangane da Mahaifinka?

Jawad Nasrallah: Abinda nafiso kasancewarsa mahaifina!

Yaushe ne haɗuwar ku ta qarshe kafin Shahadarsa?

Mun yi wata "3" bamu haɗu dashi ba!

Ta yaya kaji labarin Shahadarsa?

Naji ne nima kamar yadda kowa yaji, daga nan sai na yi ta tunanin an ciro gawar sa daga wajen ko yana ciki, sai da wani yaje wajen ya ƙira Syed Safiyudden ya tabbatar masa Sannan nima na yi
magana dashi Sai naji ya yi min ta'aziyya, duk da a lokacin Syed Hashim bai sanar ba sai da ya tabbatar an fito da gawar daga baraguzan gini!

Kaga gawar?

Eih! mun qara magana da Syed Safiyudden a lokacin akwai tunanin zasu ƙara kawowa gawar hari ko Ambulance ɗin da ke ɗauke da ita ko asibitin da aka Ajjiye ta,

Sai Syed Safiyudden ya ce naje Hussainiya "X" ko "Y" zan haɗu da wanda zai kaini inda mahaifina yake, inda naje na farko banga wanda zamu haɗu ba, Sai da naje na 2 muka tafi asibiti a lokacin naga gawar ana tsaka da binciken ko pressure da rashin iska ne s**a yi ajalinsa, daga nan kuma sai na samu nutsuwa,

Bayan kasancewarsa uba gareka me ya fi birgeka a tare dashi?

Yadda yake koya min afuwa haƙuri da juriya sannan ya tarbiyyantar dani yadda ake mu'amala da mutane!

A matsayin shi na Mahaifinka kuma jagora yana yadda da ƙalubale ko Yi masa gyara?

Sosai ma kuwa ina gaya masa ya riƙa rage kuka idan ya hau mimbari zai yi magana ni bana so masoyansa ba za suji daɗi ba ina gaya masa ya riƙa yin fara'a!

Lokacin da yana raye ku da shi yaya kuke jin irin zage-zagen da ake masa?

Mude ba abinda muke ji shima kuma haka tun da ya haddace bible old testament kuma yana karantashi harda new testament din ma yana karanta Kur'ani yasan duk wani cin mutunci da Aka yi wa Annabawa irin Musa da Isah da Annabin mu da Ahlilbait AS.

Shaheed sayeed Ahmad ibrahim zakzaky a kwance ba rai jikin sa,  Sojojin nigeria neh karkashin jagorancin kamal s. O okun...
24/04/2023

Shaheed sayeed Ahmad ibrahim zakzaky a kwance ba rai jikin sa,

Sojojin nigeria neh karkashin jagorancin kamal s. O okun s**a shahadantar da shi aranar quds ta duniya a garin zaria a shekarar 2014

Muna da masaniyar cewa duniya nan filin gwaji ce, shi ya sa muka tsaya kyam a kan tafarkin Allah, domin muna da wata man...
28/08/2022

Muna da masaniyar cewa duniya nan filin gwaji ce,
shi ya sa muka tsaya kyam a kan tafarkin Allah,
domin muna da wata manufa da muke fata cewa wata rana Allah Ta'ala Ya tabbatar da ita.

-Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H)


26/08/2022

16/08/2022

Duk yanda kakai da son kawo sauyi Dole saikayi karatu A tafiyar nan ta malam zakzaky.

Isihaq yusup.

zainab qaseem sulaimany ta cigaba da cewa, mahaifinmu bayan cushewar ayyuka da kullum-kullum yake fama dasu, akwai wani abu daya shigar dashi daga cikin wajibansa na kullum-kullum kamar sallah shine karatuttuka, kuma inda yafi maida hankali akai shine siyasar duniya, tarishin yake-yake, da al'ummun da aka samu sauyi a cikinsu da ilimin zube a yaren farinsanci, sannan yana ajiye kebataccen littafi dayake rubuta dukkan abu mai muhimmancin daya tsinta a ciki, wannan wajibi haka ya maidashi a kullum.

Akwai wata dama da wannan Abin yabashi, sau dayawa qaseem sulaimany idan aka kawo case ko wani opperation daza ai, akan jinkirta aji mai zaice saboda kwarewa a iya kawo mafitar dazata bulle babu 'opperation failure' haka aka ringa tababa dashi akan generorin Taliban a Afghanistan karshe dayawa wasu s**a tuba wasuma s**a shiga jerin gwanon Quds Force, saboda yana wahala ka kawo masa case qaseem sulaimany baitaba karanta irinsa a littafiba kuma ya bibiyi mafitsrsa.

Sanda mallcom X, aka kaishi prison bai iya komai ba, babu Rubutu b***e karatu, kuma shauqi da son canza yanayin Al'umma ya aureshi, A tsawon wannan shekarun dayayi ya riski hasken matakin farko ya rungumi littafi da alkalami, karshe mallcom X, har iran yaje, haka ma Martin Luther King, Douglas da che duk karatune matakin farko a nasararsu.

16/08/2022

ADALCIN UBANGIJI

Wata mata ta je gurin Annabi Dauda (AS) cikin fushi, ta ce masa "Ya Annabi Allah! Ubangijinka yana da adalci kuwa"?
Sai ya ce: "Kwarai kuwa, mai adalci ne, ba ya zalunci. Menene labarin ki"?

Sai ta ce: "Ni bazawara ce, ba ni da mai taimaka min, ga 'ya'ya mata guda 3 marayu. Ina ciyar da su ne da sana'anar saka da nake yi. Jiya na yi sakata mai yawa, na daure a wani jan tsumma, zan tafi kasuwa na sayar, na sami abin da zanciyar da kaina da 'ya'yana, sai wani tsuntsu ya zo ya wafce daga hannuna. Kuma ba ni da komai, ga marayu.

Kafin Annabi Dauda (AS) ya ce komai ga wannan mata, sai ga wasu mutane su 10 sun shigo, kowannen su da Dinare 100 a hannunsa, s**a ce "Ya Annabi Allah! Muna son za mu yi sadaka da wannan kudine gaba daya.

Sai Annabi Dauda (AS) ya ce dasu "ko me ya faru?" sai s**a ce "Muna cikin jirgin ruwa, sai iska mai karfi ta taso, jirgin namu ya bule, sai muka dinga ambaton Allah, kuma muka yi Bakancen idan Allah Ya tseratar da mu, za mu yi sadaka da Dinare dari-dari muna cikin wannan hali, sai gawani tsuntsu ya jeho mana wani jan tsumma, a cikin tsumman akwai wata saka Sai muka toshe bular da wannan sakar, Allah ya tseratar da mu.

Sai Annabi Dauda (AS) ya yi godiya ga Allah, ya Kalli wannan mata ya ce mata "Ubangijinki mai adalci ne, idan kin yi sakar nawa k**e siyarwa?"Sai ta ce"Dirhami daya". Sai ya ce "to ga Dinare Dubu 1000, Allah Ya sayi sakarki, karbi ki je ki ciyar da 'ya'yanki".

Allahu Akbar Ya Allah kawarware mana dukkan matsalolinmu ka yalwatamana arzikinmu kabudamana kofofin samummu, katsawaita rayuwarmu akan yimaka biyayya karshen Mu yazama shahada saboda Allah.

14/08/2022

TAQAICECCEN TAARIHIN MALAMA ZEENATUDEEN.

Nasabar malama zeenatu:ita 'yace ga malam ibaraheem, da malama marayam.

Anhaifeta ne ranar 14/8/1961, unguwar sabon gari zaria,

Su hudu a wurin mahaifiyarsu, Nafisa ibraheem, maryam ibraheem, zeenatudeen ibaraheem, khadija ibraheem,

Karatunta: Ta fara karatun firamare a mishon da take sabon gari, daga baya ta koma firamare jafaru, wato st, george primary school zaria, daga 1967 zuwa 1973. daga nan ta tafi COMMERCIAL COLLEGE ZARIA, a shekara ta 1977, ta kammala a 1979, sai ta tafi CAST katsina tayi shekara 2, a can daga nan sai ta shiga JAMI'AR AHMAD BELLO ZARIA, inda take karanta fannin aikin banki amma bata samu damar karasawa ba sakamakon korasu da makarantar tayi saboda harkokin Addini a shekara ta 1982. Daga nan malama zeenat ta tafi karatu, HAUZA ILMIYYAH, dake qasar IRAN, daga shekara ta 1982, zuwa 1984.

Malama zeenat baiwar allah ta tsaya qyama a tafarkin Addini, domin duk abinda take dashi ta bayar wa addini.

Wanna a taƙaice kenan.

Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana Umush_Shuhada.🤲

Happy Birthday Ummar mu.
🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂

13/08/2022

-YADDA SHAHADAR SAYYADA SUKAINA TA KASANCE.

-Innalillahi Wa Inna llaihi Raji'un! Tarihin Wannan Ƙaramar Yarinya Mai Suna Sakina Yana Girgiza Zukatan Muminai Sosai, Malam Kowanne irin Addini Kake yi ldan Kaji Labarin Wannan Yarinya Sai Ka Tausaya Mata.

-Sayyada S**aina Ta Kasance Ƴa Ce ga Imam Hussain Kuma Sun Shaƙu Sosai da Imam Hussain (AS), Bayan An Kashe Imam Hussain da Sauran Jikokin Manzon Allah da Dukkan Sahabban Imam Hussain, Sai Aka K**a Mata da Ƙananan Yara Amatsayin Ganimar Yaƙi.

-Lokacin da Aka Kawo wa Sarki Yazidu (LA) iyalan Gidan Manzon Allah (S) Amatsayin Ganimar Yaƙi, Sai Ya Bada Umarnin Akai Dukkan Ƴaƴan Manzon Allah (S) Kurkukun da Ya fi Kowanne Tsanani da Muni, Kuma Idan An Kaisu A Sanya su A Ɗakunan Ƙarƙashin Ƙasa.

-Allahu Akhbar lta Kuma Sayyada Sakina Yarinya Ce Ƙarama Ƴar Shekara Biyar ta kan Gagara Yin Barci Saboda Tunanin Babanta, Wani Lokaci A Cikin Tsakiyar Dare Sai Sakina ta Farka ta K**a Rusa Kuka da Ƙarfi, Tana Neman Babanta, Tana Cewa Ina Babana! Akai Ni Wurin Babana.

-Sai Aka yi ta Rarrashinta Ana ta Bata Haƙuri Amma Ina Sai ma Ƙarawa Take yi, Sai ta Cewa Sayyada Zainab (AS) "ina Babana Yake? Yanzunnan Muna Tare Dashi Har Ya Sumbance Ni Yace Min An Jima Kaɗan Zan Kasance Tare Dashi, Amma Gashi Yanzu Kuma Ban Ganshi Ba!

-Da Jin Haka Sai Duk S**a K**a Kuka, Lokacin da Kuka Yayi Yawa Sai Yazidu (LA) Ya Turo Wani Bawansa Ya Tambaya Menene Ya Faru? Sai Aka Faɗa Masa Cewa Sakina Ce Ƴar Hussain Take Kuka Tana Neman Babanta.

-Sai Yazidu Yasa Aka Kawo wa Sakina Yankakken Kan Babanta A Cikin Faranti Sai ta Rungume Kan da Ƙarfi Tana Kuka Tana Cewa Waye Ya Cire Kan Babana? Bayan Wani Lokaci Sai Aka ji Ta yi Shiru, Duk An yi Tsammanin Ta yi Barci Ne, Inna lillahi Wa Inna ilaihi Raji'un!!!

-Ashe Ita Sayyada S**aina Tayi Barcin Din-Din-Din Ne, Anan Ta Rasu Tana Rungume da Kan Babanta.

-ASSALAMU ALAIKI YA SAKINA YA MAZLUMA!!!

-Allah Ya Saka Muku Abisa Zaluncin da Aka yi Muku.

-Muhammad Jiddah Nguru

13/08/2022

MUN FAHIMCI WANNAN KUWA? :

"Makiya ba taron Ashura suke tsoro ba, darasin tawaye ga azzaluman da taron Ashura ke koyarwa suke jin tsoro."

KUMA HAKA ZAMU CIGABA DOMIN:

"Kowacce rana Ashura ce, kuma kowanne guri Karbala ce."

~Imam Khomaini (Q.S)
Shugaban Juyin Juya
Halin Musulunci na
Kasar Iran.

12/08/2022

An kai wa Salman Rushdie hari a birnin New York bayan ya shafe tsawon shekaru yana buya sakamakon batanci ga Annabi.

Marubucin mai shekara 75, wanda ya lashe kyautar The Booker Prize, yana jawabi ne a Cibiyar Chautauqua yayin da aka kai masa hari.

Ganau sun ce sun ga wani mutum ya ruga a guje ya hau kan dandamalin da marubucin yake jawabi inda ya rika naushi yana kuma daba wa Mr Rushdie wuka a yayin da ake gabatar da shi gaban jama'a.

Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan intanet ya nuna mahalarta taron sun ruga a guje kan dandamalin don kai masa dauki.

Bayanai sun nuna cewa akwai alamun an daba masa wuka a wuya.

An garzaya da shi wani asibiti a cikin helikwafta, ko da yake babu cikakken bayani game da girman raunin da aka ji masa.

Allah ya kare mu da aikata da na sani
11/08/2022

Allah ya kare mu da aikata da na sani

Ana zargin wata mata da kashe 🔪 mijin abokiyar maɗigonta 👩‍❤️‍👩 a Anambra

Domin karanta cikakken labarin, bude wannan (☞゚ヮ゚)☞ https://bbc.in/3Qg2mIR

'Yan Uwa Na Jama'are Sunyi Addu'o'in Musamman Ga Shahidan Ashura 1444Da yammacin yau alhamis ne wasu ba'adin 'yan uwa mu...
11/08/2022

'Yan Uwa Na Jama'are Sunyi Addu'o'in Musamman Ga Shahidan Ashura 1444

Da yammacin yau alhamis ne wasu ba'adin 'yan uwa musulmi almajiran Shaikh Zakzaky (H) na da'irar Jaa'are, s**a hadu a fudiyya Jama'are, s**a kuma gabatar da addu'ar uku ga shahidan Ashura shida (6) na wannan shekarar da aka samu a Zariya

A lokaci guda kuma, s**a hada da yiwa matar wakilin 'yan uwa almajiran shaikh Zakzaky na Azare, Marhuma Malama Khadeeja Abdullahi da Allah yayiwa rasuwa ranar labara da ta gabata addu'ar Allah ya mata gafara, ya yafe mata kurakurenta, ya kuma sadar da ita ga sayyidush shuhada Imamu Hussaini

✍El-Mu'az Jama'are
'areMediaForum

Address

Kaduna

Telephone

+2347064496659

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muryar masu rauni posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Muryar masu rauni:

Share