Avverh Gentle

Avverh Gentle PROBLEM SOLVER IN POULTRY FARM 👳🧑‍🎓
DÅRRÛSSÁN KÎWØ 👑 🐔
ÉNTRËPRĒNÊUR💪💰
C.E.O GENTLE ENTERPRISES 💯📌

ASTAGFIRULLAH-WA'ATUBI'ILAIK YA ALLAH 🙏🙏🙏

Am Avverh Gentle muslim
Allah
Rasulullah
Qur'an

28/04/2026

Ba'a Kunnawa Kaji🐔 Maganin Sauro.
Don Yana Sasu Mura
Akiyaye👂

ANTIBIOTICS NEUFURAMACY:-Wannan Neufuramacy kenan Antibiotic ne Yana magance:- Zawo kashin ruwa, Cutar ciki enteritis, M...
28/04/2026

ANTIBIOTICS NEUFURAMACY:-
Wannan Neufuramacy kenan Antibiotic ne Yana magance:- Zawo kashin ruwa, Cutar ciki enteritis, Matsalar numfashi respiratory infections, Wasu cututtukan bacteria da ke rage girman kaji Da Sauransu.

Don Kasancewa damu Akan shawarwari da ingantun Darussanmu sai Ku Kasance Damu a Sabon WhatsApp Group Dinmu shiga Naira 1000 Kacal Ga Mai Bukata Yayimin magana ta WhatsApp:-
09127823934.
Avverh Gentle 😎🐔✍️❤️

MULTIVITAMIN NA KAJIVitranor magani ne da ake amfani da shi a kiwon kaji (da sauran dabbobi), kuma multivitamin ne Mai k...
27/04/2026

MULTIVITAMIN NA KAJI
Vitranor magani ne da ake amfani da shi a kiwon kaji (da sauran dabbobi), kuma multivitamin ne Mai kyau
Me yake yi?
Vitranor yana taimakawa: Kara ƙarfi da lafiya ga kaji. Rage stress misali lokacin zafi ko bayan rigakafi. Taimakawa wajen girman broilers da sauri. Inganta egg production a layers. Gyara rashin bitamin Wato vitamin deficiency.

Don Kasancewa damu Akan shawarwari da ingantun Darussanmu sai Ku Kasance Damu a Sabon WhatsApp Group Dinmu shiga Naira 1000 Kacal Ga Mai Bukata Yayimin magana ta WhatsApp:-
09127823934.
Avverh Gentle 😎🐔✍️❤️

MULTIVITAMIN NA KAJI Esmovita magani ne da ake amfani da shi a kiwon kaji domin ƙara lafiyar su da taimaka musu su jure ...
27/04/2026

MULTIVITAMIN NA KAJI
Esmovita magani ne da ake amfani da shi a kiwon kaji domin ƙara lafiyar su da taimaka musu su jure cututtuka. Ba lallai ba ne ya zama maganin cuta kai tsaye, amma yana aiki ne a matsayin vitamin da rigakafin ƙarin ƙarfi da gina jiki.
Amfanin Esmovita ga kaji:
Yana ƙara ƙarfi da kuzari.
Yana taimakawa kaji su ci abinci sosai su yi girma da sauri.
Yana rage stress musamman bayan rigakafi ko safara.
Yana taimakawa wajen ƙarfafa garkuwar jiki.
Yana taimaka wa kaji su murmure bayan rashin lafiya.

Don Kasancewa damu Akan shawarwari da ingantun Darussanmu sai Ku Kasance Damu a Sabon WhatsApp Group Dinmu shiga Naira 1000 Kacal Ga Mai Bukata Yayimin magana ta WhatsApp:-
09127823934.
Avverh Gentle 😎🐔✍️❤️

27/04/2026

Tambaya:-
Shin Ana Hada Antibiotic da Multivitamin?
Amsa:-
👇👇👇👇👇

26/04/2026

Da Fatan Kun Fara Bawa Kajinku🐔 Ganyen Gwanda 🍀.
Gentle ✍️🐔

DARASIN YAU:-GANYEN GWANDA GA KAJINMUGanyen gwanda na daya daga cikin ƙarin abinci na Gargajiya mai arha da ake bai wa k...
25/04/2026

DARASIN YAU:-
GANYEN GWANDA GA KAJINMU

Ganyen gwanda na daya daga cikin ƙarin abinci na Gargajiya mai arha da ake bai wa kaji, wanda ke ƙarfafa garkuwar jiki, yana aiki a matsayin maganin tsutsotsi na Gargajiya, kuma yana taimakawa hana cutar coccidiosis. Saboda yana ɗauke da sinadarin papain, yana inganta narkewar abinci, yana ƙara nauyin broilers, da kuma ƙara yawan ƙwai a kajin layers. Anfi ba da shi ta hanyar busar da shi a niƙa a haɗa da abinci ko kuma a fitar da ruwan ganyen a haɗa da ruwa abasu.

MUHIMMAN AMFANIN LAFIYA
1.
Rigakafin Coccidiosis:
Yana taimakawa sarrafa kamuwa da ƙwayoyin parasites, yana rage buƙatar amfani da magungunan sinadaran chemical.

2.
Maganin Tsutsotsi na Gargajiya:
Yana rage yawan tsutsotsi a jikin kaji.

3.
Ƙara Girma:
Yana taimakawa broilers su ƙara nauyi, kuma yana ƙara yawan ƙwai ga layers.

4.
Yanada Arzikin Sinadarai:
Yana ɗauke da sinadarai da ke inganta lafiyar kaji gaba ɗaya, garkuwar jiki, da amfani da abinci yadda ya kamata.

Yadda Ake Shirya da Amfani da Ganyen Gwanda
A.
Hanyar Busarwa (Mafi Kyau):
A busar da ganyen gwanda a inuwa na kusan mako guda, sannan a murƙushe su su zama ƙanana wato adaka. A haɗa wannan garin da abinci da kashi gram 15 a cikin kilo 1 na abinci, ko kuma gram 400 a cikin kilo 100 na abinci.

B.
Hanyar Ruwan Ganye:
A wanke sabbin ganyen Gwanda, sannan a daka, a markada, sai a matse su domin fitar da ruwan. A haɗa ruwan da ruwa ruwan Gwanda ya zama Kashi 1 bisa uku na ruwan da zaa hada da shi.

Yadda Ake Ba Su:
A ba kaji aƙalla sau biyu a mako, a fara daga sati biyu da haihuwa.

Abubuwan Lura
Kada a Abasu sabbin ganye gaba ɗaya domin ɗacin su na iya rage cin abinci.
Kada a dogara da shi a matsayin cikakken abinci ko magani don shi rigakafi ne Kuma kari ne kawai. Duk da yana iya zama madadin antibiotics, yana da amfani sosai a matsayin rigakafi ne.

Don Kasancewa damu Akan shawarwari da ingantun Darussanmu sai Ku Kasance Damu a Sabon WhatsApp Group Dinmu shiga Naira 1000 Kacal Ga Mai Bukata Yayimin magana ta WhatsApp:-
09127823934.
Avverh Gentle 😎🐔✍️❤️

25/04/2026

Yau Zamuyi Darasin Ganyen Gwanda Ga Kajinmu
In Sha Allah.
Avverh Gentle ✍️

DARASIN ANJIMA:-GANYEN GWANDA GA KAJIIn Sha Allah Anjima Da Yamma Zamuyi Darasin Nan Duk Muntaba Yi Amma Zamuyi Saboda Y...
23/04/2026

DARASIN ANJIMA:-
GANYEN GWANDA GA KAJI
In Sha Allah Anjima Da Yamma Zamuyi Darasin Nan Duk Muntaba Yi Amma Zamuyi Saboda Yan Yadda Kajinmu S**a Dan Tasa Akwai Bukatan Ayi Darasin Don Fara Amfani Dashi Duk da Nasan Wanda S**a San Amfaninsa Already sun Fara Amfani Dashi.
In Sha Allah Zamuyi Zuwa Anjima Awannan Page Din Namu Mai Albarka

Don Kasancewa damu Akan shawarwari da ingantun Darussanmu sai Ku Kasance Damu a Sabon WhatsApp Group Dinmu shiga Naira 1000 Kacal Ga Mai Bukata Yayimin magana ta WhatsApp:-
09127823934.
Avverh Gentle 😎🐔✍️❤️

22/04/2026

Kusan Duk Mutuwan Kaji Da Rashin Girmansu ayanzu Dalilin Zafine Don Haka Akula Da Zafi.
Gentle ✍️🐔

22/04/2026

Baayin Allura Ga Kaji Da Rana Sai Da Safe Ko da Yamma.
Amfison Ayi Da Safe Karfe 6 - 10 na safe.
Gentle 😎🐔

22/04/2026

Ku Aje Mana Matsalolin dakuke Fuskanta akiwo Don Yin Darasin anji Akan Wanda Yafi yawa.
👇👇👇👇

Address

Igabi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Avverh Gentle posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share