Darul Hadeeth Wal-Fiqhu

Darul Hadeeth Wal-Fiqhu Anbude Wannan Shafi ne Domin Samun Karatukan Maluman Sunnah Daban-Daban A Fadin Afirka.

Jiya na ji wani kasurgumin makaryaci Dan Bidi'a yana yi wa Ahlus-Sunnah sharri, yana cewa ba su taɓa yin wata lacca mai ...
29/10/2025

Jiya na ji wani kasurgumin makaryaci Dan Bidi'a yana yi wa Ahlus-Sunnah sharri, yana cewa ba su taɓa yin wata lacca mai taken “Son Annabi Muhammad ﷺ” ba.

Wannan ƙarya tasa ta tunatar da ni karatun littafin Ash-Shifā, wanda Sheikh Abdurrazaq Haifan (hafizahullah) yake karantawa. A cikin darussa na 002 da 003, Malamin ya gabatar da karatun mai taken “Ayoyin Ɗaukakar Annabi ﷺ.”

Ina roƙon duk mai son gaskiya da neman ilimi da ya samu lokaci ya saurari waɗannan darussa guda biyu (tsawon sa’o’i biyu kacal). Zai ga yadda Malamin ya yi bayani mai zurfi, cike da ƙauna, ladabi da girmamawa ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.

Lallai, waɗannan karatun suna ƙara haske ga zuciya, suna kuma ƙarfafa soyayya da biyayya ga Annabi ﷺ, wanda shi ne ginshiƙin addininmu.

27/09/2025

Ga wasu muhimman darussa guda 10 daga babban Malami Ibnul Qayyimul Jawziyyah. A daure a karanta za'a samu fa'ida.

1. Game da zuciya:

> “Zuciya tana rayuwa da zikiri kamar yadda jiki yake rayuwa da ruwa.”

2. Game da zunubi:

> “Zunubi yana barin duhu a cikin zuciya, idan aka ƙara zunubi sai duhun ya ƙaru, har sai zuciya ta mutu.”

3. Game da addu’a:

> “Addu’a ita ce makamin mumini, ita ce tsari daga kowanne sharri.”

4. Game da rayuwa:

> “Duniya kamar mafarki ce, mai hankali shi ne wanda yake aiki don lokacin farkawa (lahira).”

5. Game da soyayya:

> “Duk abin da aka so saboda Allah, ba zai ƙare ba; duk abin da aka so ba don Allah ba, zai lalace.”

6. Game da natsuwa:

> “Babu wani abu da ke kawo natsuwa ga zuciya kamar Qur’ani.”

7. Game da ilimi:

> “Ilimi shi ne abincin zuciya, kuma istighfari shi ne maganinta.”

8. Game da zaman duniya:

> “Duniya ba gida ba ce, gida wurin tafiya ce. A lahira ne gida.”

9. Game da sabr (haƙuri):

> “Dukkan nasara tana tare da haƙuri, kuma haƙuri shi ne ginshiƙin imani.”

10. Game da Allah:

> “Duk wanda ya dogara ga Allah, Allah zai wadatar da shi. Duk wanda ya dogara ga kansa, zai rasa.”

04/09/2025

Takaitaccen bayani akan Sheikhul Islam Ibn Taymiyyah.

Sheikhul Islam Ibn Taymiyyah shi ne Taqiyuddin Ahmad Ibn AbdulHalim Ibn Abdussalam Ibn Taymiyyah al-Harrani (1263–1328 Miladiyya).

Ga takaitaccen bayani a kansa:

Asali da haihuwa: An haife shi a garin Harran (a kasar Sham, yanzu Syria), a shekara ta 661H (1263M).

Karatu da Ilimi: Ya girma cikin iyali na malamai, ya haddace Alkur’ani da wuri, ya zurfafa cikin Hadisi, Tafsiri, Fiqhu, Luga, da falsafa.

Sana’arsa: Malamin addini ne, mai fassara Alkur’ani da Hadisi, da kuma babban mai kare akidar Ahlus-Sunnah.

Sunansa “Sheikhul Islam”: Wannan lakabi ne da malaman Musulunci s**a yi masa saboda tsantsar iliminsa da jajircewarsa wajen kare akidar Musulunci.

Ayyukansa: Ya rubuta littattafai da dama (misali Majmu’ al-Fatawa, Dar’ Ta’arud al-‘Aql wa an-Naql, da As-Siyasah ash-Shar’iyyah).

Kokarinsa: Ya yi yaƙi da bidi’o’i, kuskuren falsafanci da sufaye, da kuma duk wani abu da yake ganin ya sabawa koyarwar Qur’ani da Sunnah. Ya kuma taka rawa wajen karfafa Musulmi a lokacin mamayar Mongolawa.

Rashin Lafiya da Mutuwa: Saboda tsayuwarsa kan gaskiya, sau da dama aka tsare shi a kurkuku. A lokacin yana kurkuku a Damasko ne ya rasu, a shekara ta 728H (1328M).

An san Ibn Taymiyyah da tsantsar imaninsa, ilimi mai zurfi, da karfin hujja, har yanzu tasirinsa yana da karfi a tsakanin malaman Musulunci.

Mutane da dama a ƙasashen Faransa, Girka, Pakistan da dai sauran su sun fito domin yin alla-wadai da harin da Amurka ta ...
23/06/2025

Mutane da dama a ƙasashen Faransa, Girka, Pakistan da dai sauran su sun fito domin yin alla-wadai da harin da Amurka ta kai kan Iran a wani ɓangare na rikicin Isra'ila da Iran.

A birnin Washington DC, ɗaruruwan mutane sun je gaban fadar shugaban Amurka domin nuna rashin amincewarsu da matakin na Trump.

Trump dai ya ce "ya kai harin ne kan cibiyoyin sarrafa makamashin nukiliya na Iran domin daƙile yunƙurin ƙasar na mallakar makamin nukiliya".

~BBC HAUSA.

13/04/2025

Alamar son Annabi S.A.W

14/03/2025

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Fau Zhia, Abdul Abu Anas

01/03/2025

Jama'a barkanmu da arzikin ganin wannan lokaci mai tarin Albarka.

Wannan dama ce ba karama ba, Allah mun gode ma ka, bisa wannan ni'ima.

Allah ka karbi dukkanin ibadun da za mu gabatar, ka yafe mana dukkan kura-kuranmu.

13/09/2024

Allah ka sa mu yi karshe mai kyau, Don Alfarmar Sayyidina Rasulullah S.A.W

Address

Abubakar Gumi Street
Funtua
KT-NG

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Darul Hadeeth Wal-Fiqhu posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Practice

Send a message to Darul Hadeeth Wal-Fiqhu:

Share

Category