Barr. Usman Saeed Maikeke

Barr. Usman Saeed Maikeke Driven by integrity, justice, and service to the people, he is c

Barrister Usman Saeed Maikeke is a dedicated legal practitioner and Political Candidate contesting for the Kano State House of Assembly, representing Fagge Local Government Area, Kano State.

Jama’ar al'ummar karamar hukumar Fagge  mai albarka, ina yi muku fatan alkhairi gaba ɗaya.Ina miƙa godiyata ta musamman ...
27/04/2026

Jama’ar al'ummar karamar hukumar Fagge mai albarka, ina yi muku fatan alkhairi gaba ɗaya.
Ina miƙa godiyata ta musamman bisa irin goyon baya da ƙwarin gwiwar da kuke ci gaba da bani a wannan tafiya. Lallai, da ba ku ba, da wannan tafiya ba za ta samu wannan nasara ba.
Ina ƙara roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya saka muku da alkhairi, Ya ba mu nasara, Ya kuma ƙara haɗa kanmu da zumunci a tsakaninmu. Allah Ya ba mu lafiya da zaman lafiya, Ya kuma ba mu ci gaba mai ɗorewa da albarka a ƙaramar hukumar mu ta Fagge.
FAGGE ITACE KAN GABA A MURADUNMU!
Naku,
Hon. Barr. Usman Sa’idu Maikeke

SAƘON TA’AZIYYABarrister Usman Sa’eed Maikeke yana miƙa saƙon ta’aziyyarsa bisa rasuwar dattijo, uba, kuma tsohon shugab...
19/04/2026

SAƘON TA’AZIYYA
Barrister Usman Sa’eed Maikeke yana miƙa saƙon ta’aziyyarsa bisa rasuwar dattijo, uba, kuma tsohon shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa, Alhaji Ibrahim Galadima na Fagge.
Wannan rashi babbar gibi ne ga al’umma, musamman a fannin ƙwallon ƙafa da hidimar jama’a, duba da irin gudunmawar da marigayin ya bayar tsawon rayuwarsa.
Muna roƙon Allah (SWT) ya jiƙansa da rahama, ya gafarta masa kura-kuransa, ya kuma saka masa da Aljannatul Firdausi. Allah ya ba iyalai, ‘yan uwa da daukacin al’umma haƙurin jure wannan babban rashi.
Amin.

Mai Girma Hon. Barr. Usman Sa’idu Maikeke, ɗan takararmu na Majalisar Jiha, yana miƙa saƙon ta’aziyya ga H.E. Nasiru El-...
29/03/2026

Mai Girma Hon. Barr. Usman Sa’idu Maikeke, ɗan takararmu na Majalisar Jiha, yana miƙa saƙon ta’aziyya ga H.E. Nasiru El-Rufa’i da kuma Jam’iyyar ADC baki ɗaya bisa wannan babban rashi na rasuwar mahaifiyarsa.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da ya jiƙanta da rahama, ya gafarta mata, ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarta. Allah kuma ya jiƙan dukkan magabatanmu, ya kuma kyautata tamu zuwan.
Amin.
Saƙo daga:
P.A na Honorable kan yaɗa labarai

Sakon Barka da Sallah daga Barrister Usman Saeed MaikekeDa sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai, ina miƙa sakon Barka da S...
20/03/2026

Sakon Barka da Sallah daga Barrister Usman Saeed Maikeke
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai, ina miƙa sakon Barka da Sallah ga daukacin al’ummar Musulmi yayin da muke bikin Eid al-Fitr bayan kammala azumin watan Ramadan.
Ina roƙon Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya gafarta mana kura-kuranmu, Ya kuma sa wannan rana ta zama ta farin ciki, zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’ummarmu.
A wannan lokaci mai albarka, ina kira ga jama’a da mu ci gaba da kasancewa masu tausayi da taimakon juna, musamman ga marasa galihu, marayu da masu buƙata. Hakan shi ne darasin da watan Ramadan ya koyar da mu.
Allah Ya sa wannan Sallah ta zo mana da alheri, Ya kuma maimaita mana irin ta cikin koshin lafiya, zaman lafiya da wadata.
Barka da Sallah!

15/03/2026

Na samu halartar bikin rufe karatun Ashafa na Mal. Kamal Mai Jabari da aka gudanar a Fagge.

Juma'at Mubarak
06/03/2026

Juma'at Mubarak

BARKA DA SHAN RUWAAssalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu.Ina mika sakon Barka da Shan Ruwa ga daukacin al’ummar ...
24/02/2026

BARKA DA SHAN RUWA
Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu.
Ina mika sakon Barka da Shan Ruwa ga daukacin al’ummar Musulmi. Ina rokon Allah (SWT) Ya karbi azuminmu, ya karbi ibadunmu, ya gafarta mana kura-kuranmu, ya sanya mu cikin bayinsa nagari.
Allah Ya ba mu lafiya da zaman lafiya a kasarmu, Ya yalwata arziki, Ya kawo mana karshen duk wata matsala da take addabar al’umma.
Barka da Shan Ruwa, Allah Ya maimaita mana cikin koshin lafiya da imani.
Barrister Usman Saeed Maikeke

Ramadan Mubarak
17/02/2026

Ramadan Mubarak

🕌 SAKON BARKA DA JUMA’A 🕌Mai Girma Barr. Usman Sa’eed Maikeke na taya daukacin al’ummar musulmi murnar sake zagayowar wa...
13/02/2026

🕌 SAKON BARKA DA JUMA’A 🕌
Mai Girma Barr. Usman Sa’eed Maikeke na taya daukacin al’ummar musulmi murnar sake zagayowar wannan rana mai albarka ta Juma’a.
Yana kira gare mu da mu kara kusantar Ubangiji ta hanyar yawaita istigfari, salati ga Annabi Muhammad (SAW), da kuma aikata ayyukan alheri domin samun rahama da gafara.
Muna rokon Allah (SWT) Ya wadata kasarmu da zaman lafiya, Ya hada kanmu, Ya kuma albarkaci dukkan ayyukanmu na alheri.
Allah Ya sa mu dace da falalar wannan rana, Ya amsa mana addu’o’inmu.
Juma’a Mubarak 🌙

A daren Lahadi, 08/02/2026, Mai Girma Hon. Barr. Usman Sa’idu Maikeke ya halarci bikin kammala Musabakar Alƙur’ani da ak...
10/02/2026

A daren Lahadi, 08/02/2026, Mai Girma Hon. Barr. Usman Sa’idu Maikeke ya halarci bikin kammala Musabakar Alƙur’ani da aka gudanar a Unguwar Fagge, wanda Ƙungiyar Makarantun Islamiyyoyi na Kwaryar Fagge s**a shirya.
A yayin taron, Ƙungiyar ta karrama Mai Girma Hon. Barr. Usman Sa’idu Maikeke da Kyautar Girmamawa, bisa gudunmawarsa da jajircewarsa wajen tallafawa harkokin addini da ilimi a al’umma.
Muna addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara musu ƙwazo da kwarin gwiwa wajen ci gaba da aikata ayyukan alkhairi, Ya kuma sanya Alƙur’ani ya zamo haske, shiriya da albarka gare mu baki ɗaya. Amin.

A ranar Asabar, 08 ga Fabrairu, 2026, Mai Girma Hon. Barr. Usman Maikeke ya kai ziyarar jaje da nuna tausayi ga Alhaji M...
09/02/2026

A ranar Asabar, 08 ga Fabrairu, 2026, Mai Girma Hon. Barr. Usman Maikeke ya kai ziyarar jaje da nuna tausayi ga Alhaji Munzali Mazaf, Shugaban Kamfanin MAZAF, tare da ’yan kasuwar Singa, sakamakon ibtila’in gobara da ya auku a wasu rukunin shaguna da ke Kasuwar Singa, Jihar Kano.
A yayin ziyarar, Mai Girma ya jajanta wa waɗanda lamarin ya shafa, inda ya bayyana alhininsa bisa asarar da aka yi, tare da jaddada muhimmancin haƙuri da dogaro ga Allah Maɗaukakin Sarki a irin wannan lokaci na jarabawa. Haka kuma, ya yi addu’ar Allah Ta’ala Ya mayar da asarar da alkhairi, Ya ƙara musu juriyar zuciya, sannan Ya kare afkuwar makamancin wannan ibtila’i a nan gaba.
Ziyarar ta nuna jajircewar Mai Girma wajen kasancewa tare da al’umma a kowane hali, musamman a lokutan ƙalubale da jarabawa.
Allah Ta’ala Ya kiyaye gaba, Amin.

Address

Kurna Tudun Bojuwa
Fagge

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Barr. Usman Saeed Maikeke posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share