Hisbah Command CHAM

Hisbah Command CHAM Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Hisbah Command CHAM, Legal, Kindiyo ward Cham chiefdom, Chum.

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta sanar da haramta gudanar da sana'ar tura fina-finai a faɗin jihar nan.Mukaddashin babban ...
17/07/2026

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta sanar da haramta gudanar da sana'ar tura fina-finai a faɗin jihar nan.

Mukaddashin babban kwamandan hukumar, Dr Mujahiddin Aminuddeen, ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin hukumar na tabbatar da bin dokoki da kuma kare ɗabi'u da tarbiyyar al'umma.

Ya yi gargaɗin cewa hukumar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar matakin doka kan duk wanda aka samu yana ci gaba da gudanar da sana'ar tura fina-finai duk da wannan umarni.

A cewarsa, hukumar za ta hukunta duk wanda ya saɓa dokar ba tare da nuna bambanci ba.

Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin wani saƙon murya da mukaddashin shugaban hukumar ta jihar Kano, Dr Mujahiddin Aminuddeen, ya aikewa kafafen yaɗa labarai.



Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un 😭Allah yasa karshen wahalan kenanAllah yasa mutuwa hutuce Allah ya bamu haqurin wanna...
05/06/2026

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un 😭
Allah yasa karshen wahalan kenan
Allah yasa mutuwa hutuce
Allah ya bamu haqurin wannan rashin

Kwamishinan Hisba a jihar Bauchi ya shaida wa BBC cewa matasan biyu waɗanda shekarunsu ba su wuce 30 ba, sun nemi wani l...
22/05/2026

Kwamishinan Hisba a jihar Bauchi ya shaida wa BBC cewa matasan biyu waɗanda shekarunsu ba su wuce 30 ba, sun nemi wani limamin ya ɗaura musu aure a kan sadaki 'ƙanƙani'.

Ƙarin bayani - https://bbc.in/4nTQ0rF

SOKOTO STATE HISBAH BOARD.A yau Laraba 20/5/2026 Hukumar Hisbah ta jahar Sokoto tayi Nasarar kulle wani gida da ake aika...
21/05/2026

SOKOTO STATE HISBAH BOARD.

A yau Laraba 20/5/2026 Hukumar Hisbah ta jahar Sokoto tayi Nasarar kulle wani gida da ake aikata badala a shiyar Sokoto cilma a nan cikin birnin Sokoto tare da cafke Mutun goma Sha daya Maza da Mata.

Hakan ya biyo bayan wani samame da Jami'an Hukumar s**a kai da yammachin yau Laraba, Karkashin:
OPERATION TSAFTACE BIRNI SHEHU.

Wannan samame ya gudana ne Karkashin jagoranchin mai Girma Mukaddashin Kwamandan Hisbah na jahar Imam Sirajo Abubakar kuma
Director Da'awah and Aids

Zamu kawo maku cikakken rahoto a Vedio da zamu saki bada jimawa ba.

Gombe state Join aid group of Islam held meeting in KaltungoALLAH YA ƙara haɗa kan musulmi
19/05/2026

Gombe state Join aid group of Islam held meeting in Kaltungo
ALLAH YA ƙara haɗa kan musulmi

GOMAN FARKON NA  ZUL-HIJJAH SAƘO (22)1. Allah Madaukakin Sarki Ya Ce:“Ina rantsuwa da alfijir, da darare goma.”(Suratul ...
17/05/2026

GOMAN FARKON NA ZUL-HIJJAH SAƘO (22)

1. Allah Madaukakin Sarki Ya Ce:

“Ina rantsuwa da alfijir, da darare goma.”

(Suratul Fajr)

Ibn Kathir رحمه الله ya ce:

“Dararen goma” ana nufin goman farkon Zul-Hijjah. Haka ma Ibn Abbas, Mujahid da sauran malamai s**a bayyana.

2. Allah Ya Ce:

“Domin su ambaci sunan Allah a cikin kwanaki sanannu.”

Ibn Abbas رضي الله عنهما ya ce:

“Kwanakin sanannu” su ne kwanakin goman Zul-Hijjah.

Imam Nawawi رحمه الله ya ce:

Ana son yawaita zikiri a cikin waɗannan kwanaki fiye da sauran kwanaki, musamman ranar Arafah.

3. Manzon Allah ﷺ Ya Ce:

“Babu wasu kwanaki da aikin alheri a cikinsu ya fi soyuwa ga Allah kamar waɗannan kwanaki goma.”

4. Sahabbai S**a Tambaya:

“Ko jihadi ma bai kai ba Ya Rasulullah?”

Sai Annabi ﷺ ya ce:

“Ko jihadi ma bai kai ba, sai mutumin da ya fita da ransa da dukiyarsa sannan bai dawo da komai ba.”

5. Annabi ﷺ Ya Ce:

“Mafi alherin ranakun duniya su ne kwanakin goma.”

6. Azumin Goman Zul-Hijjah

An ruwaito cewa Annabi ﷺ yana azumin kwanaki tara na Zul-Hijjah, ranar Ashura, da kuma kwanaki uku a kowane wata.

7. Yawaita Kabbara

Ibn Umar da Abu Hurairah رضي الله عنهما suna fita kasuwa a cikin waɗannan kwanaki suna yin kabbarori, mutane kuma suna binsu da kabbarori.

Takbiran Zul-Hijjah:

Allahu Akbar, Allahu Akbar,

La ilaha illallah,

Allahu Akbar, Allahu Akbar,

Wa lillahil hamd.

8. Muhimmancin Bayyana Takbiri

Annabi ﷺ ya ce:

“Mutane ba su taru a wani wuri ba face mala’iku suna kewaye da su saboda zikiri.”

Saboda haka ana son bayyana takbiri da zikiri a gidaje, masallatai da kasuwanni.

9. Kokarin yawaita Ibada

Sa’id bn Jubair رحمه الله idan goman Zul-Hijjah s**a shiga yana ƙoƙarin ibada sosai har sai ya gaji.

10. Manyan Goma Uku

Abu Usman An-Nahdi رحمه الله ya ce:

“Salaf suna girmama wasu kwanaki goma uku:

Goman ƙarshe na Ramadan

Goman farko na Zul-Hijjah

Goman farko na Muharram”

✍️ Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Address

Kindiyo Ward Cham Chiefdom
Chum

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hisbah Command CHAM posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category