12/09/2020
:
Canzawar ruwa da muke Magana akanshi yana da kyau musan abinda ruwa yake da canzawa da shi lura da hukunce-hukuncen kowanne, kamar haka:
- : Idan ruwa ya canza kala ko dandano ko shinshina, saboda inda yake, kamar Jarkasa, Farar kasa, Kanwa, Kainuwa, Gansakuka… duk wadannan idan ruwa ya canza ya yi fari saboda wurin farar kasace ko ya yi Jaa saboda wurin jarkasace ko dandanonshi ya yi gafi saboda wurin kanwace ko tekuce ko wuraran da ake hakar mai, duk wannan canza wad a ruwa ya yi babu abinda ya shafeka zaka yi ibadarka da shi salin-alin alattacciyar ibada.
Kenan waccar Magana da aka yi sai idan ruwan ya canza da wani abu na daban da ba makwancinsaba ta yadda zai iya yuwuwa a rabasu amma a inda yake makwancinsane babu yadda za'a yi ka rabasu.
- : Idan wani abu mai tsarki kamar gishiri ko yaji ko miya ko sabulu ya zuba cikin ruwa amma kwatakwata bai canza ruwanba to wannan ruwan za'a yi ibada dashi kamar yadda bayanai s**a gabata, amma idan sun canza ruwane to wannan rowan ba za'a yi ibada da shi ba, amma za'a yi ayyukan gida da shi, kamar girki wanki kunun-zaki d.s.
- : Idan najasa ta jirkita ruwa ta daya daga cikin abubuwannan uku, to bai halatta a yi anfani da wannan rowan kwatakwata ba za'a yi ibada da shi ba, kuma ba za'a yi wasu ayyuka nadaban da shiba kenan kwararar da shi kawai za'a yi.
Lalle wannan ya nuna mana muhimmacin ruwa da kuma yadda addinin musulunci ruwa shine abinda ba yi za su ibada da shi bai sa musu feturba ko gas domin rahamar Allah ga bayinsa sai ya sanya musu ruwa kuma ya sanya shi ya zama sinadarin rayuwa. Saidai kawai idan mutum bai sami ruwaba a lokacinda zai yi tsarki sai ya yi Istijmari, ko zai yi alwala kuma gashi babu ruwa sai ya yi taimama, kamar yadda bayanansu zasu zo nan gaba.
: Daga wadannan bayanai da s**a gabata zai nuna baka yadda addinin musulunci ya baima ruwa kulawa ya kuma sawwake shi, kuma wannan yana nuna mana yadda ya zama wajibi mu tashi musan hukunce-hukuncen ruwa domin idan mutum bai sani ba sai ya debi ruwan wanki ko kuma ruwan da ya gama wanka da shi bayan ya zama sabulu ya ce zai yi tsarki da shi, domin wasu sun dauka ruwan alwala shi ake bashi wannan hukunce-hukunce amma shi tsarki mutum zai iya yi da ko wanne, alhali abin ba haka bane, Allah ya sawwake amin. Allah Shi ne masani.